Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Jarumin ya koka kan yadda ake nuna wa jarumai baƙar fata wariya a Hollywood.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Fitaccen jarumin fina-finan Hollywood, Djimon Hounsou, ya bayyana yadda yake fama da baƙin talauci duk da kasancewarsa jarumi sama da shekaru 20.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na CNN, jarumin ya bayyana cewa yana jin ana yi masa ƙwange wajen biyan albashi.

A cewarsa hakan ya sanya shi har yanzu cikin yanayin talauci duk da irin nasarorin da ya samu.

“Na shafe sama da shekaru 20 ina harkar fina-finai, na kuma lashe lambobin yabo da dama, amma duk da haka har yanzu ban yi arziƙi.

“A gaskiya, ana yi min ƙwange a albashina,” in ji Hounsou.

Jarumin ya samu nasarar fitowa a cikin manyan fina-finai irinsu Blood Diamond da In America, inda ya lashe kyaututtuka irin na Oscar.

Duk da haka, ya bayyana cewa yawancin jarumai daga Afirka ba sa samun matsayin da ya dace da su a Hollywood.

Hounsou, ya ƙara da cewa, “Duk da kasancewa ta jarumi mai fitowa a cikin manyan fina-finai, ba na samun damar da wasu ‘yan fim na wasu ƙabilu ke samu.

“Wannan babbar matsala ce ga jarumai baƙar fata a Hollywood.”

Wannan batu ya sa mutane da dama tambayar dalilin da ya sa masana’antar Hollywood ke nuna wariya wajen albashi da damar da ake bai wa jarumai baƙar fata, musamman daga Afirka.

Wasu masana sun bayyana cewa matsalar wariya a masana’antar ta jima tana shafar jarumai daga Afirka, duk da irin basirarsu.

Masana harkar fina-finai da dama sun yi kira da a yi gyara a tsarin albashi da damarmaki a Hollywood, don tabbatar da adalci ga kowa, ba tare da la’akari da asalinsu ko launin fatarsu ba.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi