Na yi shekara 9 ba na ganin mutane sai dai macizai – Amina Abdusalam
Wata matar aure mai suna Amina Abdulsama da ke zaune a garin Tulu a Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi ta ce ta yi shekara 9, ba ta ganin mutane sai dai macizai kawai. Amina Abdusalam ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu, inda ta ce, “A kowanne lokaci macizai nake […]
Wata matar aure mai suna Amina Abdulsama da ke zaune a garin Tulu a Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi ta ce ta yi shekara 9, ba ta ganin mutane sai dai macizai kawai. Amina Abdusalam ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu, inda ta ce, “A kowanne lokaci macizai nake gani, ba na ganin mutane, kuma yanzu shekara 9 ke nan ina cikin wannan hali.”
Ta ce, farkon faruwar lamarin shi ne wata rana tana zaune da rana, sai ta ga hoton fuskarta. Daga nan sai wadansu mutane suka zo da yawa. Daga nan kuma sai ta ga macizai sun fito, tun daga nan sai ba ta ganin komai sai macizai.
Tana bayyana wa danginta haka ne suka tafi Asibitin Idanu a Bauchi. Da suka je asibitin aka duba sai suka ce su ba su ga komai ba.
Amina Abdusalam ta ce sai suka dawo gida suka ci gaba da maganin gargajiya, har zuwa wannan lokaci.
Mahaifiyar Amina Abdusalam mai suna Mari Halilu ta bayyana wa wakilinmu cewa wannan al’amari ya faru ne bayan an yi mata aure. Ta ce, tana cikin wannan hali ta haifi ’ya’ya mata biyu.
Ta ce, za ta gaya maka duk abin da macizan suke yi, wani lokaci su yi ta zagaya ta, wani lokaci har sara suke kawo mata amma kai ba za ka gansu ba, kamar yadda ita ma ba za ta ganka ba.
Yayan Amina Abdusalam mai suna Muhammadu Lawal ya roki jama’a su taimaka musu da addu’a kan halin da take ciki.
Har ila yau ya roki jama’a su taimaka mata don ta ci gaba da neman magani, domin duk wani abu da suke da shi ya kare sakamakon wannan doguwar jinya da suka yi.
To, amma a zantawarsa da wakilinmu wani likitan kwakwalwa da ke a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Dokta Haruna Yakubu ya ce akwai wani ciwo da yake kama kwakwalwa, wanda yake sa mutum ya rika ji ko ganin abin da babu shi.
Ya ce, ga bayanin da aka yi, kan wannan abu da yake damun wannan mata, matsala ce ta kwakwalwa. Kuma ga bayanin da aka yi idon mataR ya mutu, amma kuma gaskiya ne za ta rika gane-ganen abubuwa.
“Sau tari idan irin wannan abu ya faru za ka ji mutane suna danganta shi da aljanu da iskoki amma ba gaskiya ba ne, domin tuni ilmin kimiyya ya riga ya yi bayanin wannan matsala. Ba wasu macizai ba ne, ta riga ta makance ne, amma saboda wannan matsala ta kwakwalwa take wadannan gane-gane,” inji shi
Dokta Haruna ya ce da za a samu mutanen da suka samu irin wannan matsala, za su dada nanata wannan bayani.
Ya ce, idan aka zo asibiti akwai magungunan da ake bai wa masu irin wannan ciwo, wadanda idan suna amfani da su za su daina wadannan gane-gane.
Wakilinmu ya kuma tuntubi Limamin Masallacin Juma’a na Unguwar Tudun Wada da ke garin Jos Ustaz Kabiru Muhammed Chidawa don jin ta bakinsa kan wannan lamari.
Ya ce, a Musulunci ana iya yi wa mutum sihiri ko mutum ya hadu da aljanu. Ya ce, a cikin Suratu Daha Allah Ya ce, suna tsorata su da sihirinsu sun juye musu idanuwansu da sanduna suka koma ganin sanda a matsayin maciji da igiyoyi.
Ya ce, don haka wannan matsala ce, ta sihiri kamar yadda Alkur’ani ya nuna. Domin an yi wa jama’ar Annabi Musa irin wannan sihiri.
Kuma duk manyan malamai sun tabbatar da cewa, akwai sihirin da ake yi wa mutum a idanu ya rika ganin wani abu daban, ba ainihin abin ba.
Ustaz Kabiru ya ce “Idan irin wannan al’amari ya faru sai mu karanta addu’o’in da Manzon Allah (SAW) ya karantar da mu. Wato mu karanta Kulhuwallahu da Falaki da Nasi sau uku da safe da yamma. Sannan mu yawaita karata surar Fatiha domin Manzon Allah (SAW) ya ce, magani ce. Sannan mu rumgumi karatun Alkur’ani, Allah zai ba da dama a warke.”