Na yi wa mahaifina alƙawarin ba zan taɓa aikata masha’a ba — Murja

Shahararriyar matashiyar nan ‘yar TikTok Murja Kunya ta bayyana takaicinta kan halin da ta tsinci kanta a ciki bayan ta gudu daga garin Kano zuwa Abuja tun bayan turka-turka da ta shiga tsakaninta da hukumar Hisbah ta jihar. Murja cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok ta bayyana cewa nisantar mahaifinta […]

Na yi wa mahaifina alƙawarin ba zan taɓa aikata masha’a ba — Murja

Shahararriyar matashiyar nan ‘yar TikTok Murja Kunya ta bayyana takaicinta kan halin da ta tsinci kanta a ciki bayan ta gudu daga garin Kano zuwa Abuja tun bayan turka-turka da ta shiga tsakaninta da hukumar Hisbah ta jihar.

Murja cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok ta bayyana cewa nisantar mahaifinta ya jefa ta cikin ƙangi na rayuwa mara misaltuwa.

Ta bayyana cewa tunda take ba ta taɓa kwashe kwana bakwai ba tare da ta ga mahaifinta ba amma yanzu yana kwance ba shi da lafiya amma ta kasa zuwa ganinsa.

Ta ƙara da cewa yanzu haka tana zaune a babban birnin tarrayya Abuja, kuma yanzu ba ta da wani buri da ya wuce na samun damar da za ta ɗauki mahaifinta ta kai shi ƙasar waje domin ya samu lafiya amma an hana ta saboda ‘buƙatar’ wasu manya a Kano.

Sai dai ta ce, kafin ta bar gida ta yi wa mahaifinta alƙawarin cewa “duk inda zan je ba zan taɓa aikata masha’a ba duk da cewa akwai manya a Kano da suke da sha’awar hakan amma na gwammace na jure duk wani matsi da tashin hankali akan ta hakan ta faru.

“Mahaifina ya min gargaɗin cewa ka da na ƙara yin wani abu da har zai kai ga hukuma ta kama ni,” a cewarta.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe