Na yi wa majinyata 15 magani — Likitan bogi

An kama wanda ake zargin, Udeme Emmanuel Ekpeme ne ta hannun jami’an ’yan sanda na shiyyar Uwanse a ƙaramar hukumar Calabar South, biyo bayan ƙorafin da wata mata mai suna Madam Edemawan Samuel ta shigar.

Na yi wa majinyata 15 magani — Likitan bogi

An kama wani mutum mai shekara 39 wanda ake zargi da yin iƙirari a matsayin likita a Jihar Kuros Riba, inda ya amsa laifin jinyar marasa lafiya aƙalla guda 15 a cikin shekaru bayan da ya bar makarantar koyon aikin likitanci.

An kama wanda ake zargin, Udeme Emmanuel Ekpeme ne ta hannun jami’an ’yan sanda na shiyyar Uwanse a ƙaramar hukumar Calabar South, biyo bayan ƙorafin da wata mata mai suna Madam Edemawan Samuel ta shigar.

Ta zarge shi da fitowa a matsayin wani sojan gona, karɓar kuɗi ta hanyar damfara, da kuma gudanar da harkar asibitin tafi-da-gidanka da kansa.

’Yan sanda sun zargi Ekpeme da damfarar matan kuɗi har Naira 500,000 bayan ya yi mata alƙawarin samar wa ’ya’yanta aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar (UCTH).

A cikin jawabin amsa laifinsa, wanda ake zargin ya ce ya bar makarantar likitanci ne, amma ya sayi kayan aikin likita da fatan tara isassun kuɗin da zai koma ya ƙarasa karatunsa.

“Idan har zan iya tara kuɗi don komawa makarantar likitanci, zan koma. Shi ya sa na sayi kayan aikin likita na gwaji domin duk lokacin da marasa lafiya suka zo, in yi amfani da su wajen gano cutar da ke damun su. Yawanci, idan marar lafiya guda ya ga maganina yana aiki, yakan ba wani shawara ya zo wajena,” in ji shi.

Ya yi iƙirarin cewa, tsakanin shekarar 2014 zuwa 2026, ya yi jinyar marasa lafiya a ƙalla 15 duk da cewa, ba shi da lasisin aikin likita.

Wanda ake zargin ya kuma amsa karɓar Naira 500,000 daga hannun mai ƙorafin kan alƙawarin ayyukan UCTH, amma ya ce ya karkatar da kuɗin ne domin biyan bashin Naira 700,000 da ake binsa.

“Dama can ina bin wani bashin Naira 700,000 kuma suna matsa min lamba in biya. Har ma sun ƙwace wayata ta Android, shi ya sa na yi amfani da kuɗin wajen biyan bashin,” cewar likitan bogi.