‘Na yi zamani da sarakunan Kano bakwai’

  Wata dattijuwa ’yar asalin kasar Yemen da ta ce ta haura shekara dari da haihuwa ta shaida wa Aminiya cewa ta san lokacin da marigayi Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Abbas yake mulki. Dattijuwar wadda har yanzu tana cin kowane irin abinci da jikokinta suke iya ci, tana gani, kuma hakoranta na nan daram: Sunanta […]

‘Na yi zamani da sarakunan Kano bakwai’

 

Wata dattijuwa ’yar asalin kasar Yemen da ta ce ta haura shekara dari da haihuwa ta shaida wa Aminiya cewa ta san lokacin da marigayi Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Abbas yake mulki. Dattijuwar wadda har yanzu tana cin kowane irin abinci da jikokinta suke iya ci, tana gani, kuma hakoranta na nan daram:

Sunanta Amina Muhammadu Ma, amma an fi saninta da Anna. Ta fito daga gidan Malam Bala na Malam Sidi da ke Unguwar Alfindiki a birnin Kano. Dattijuwar ta ce ta yi zamani da sarakunan Kano bakwai tun daga kan Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Abbas. Sarki Abbas dai ya yi sarautar Kano ne daga 1903 zuwa 1919. Wannan ya nuna cewa yanzu shakarunsa 96 ke nan da rasuwa.

Amina Muhammadu ta ce asalin kakanninta Larabawan kasar Yemen ne da suke zuwa Kano kasuwanci, daga baya ne suka zauna a Alfindiki wanda a Larabci ake kira Alfunduk da ke nufin masauki ko otal. Ta ce daga nan ne kakanninsu suka auri ’yan kasa suka gauraye da Hausawa da Fulani.
Amina ta kara da cewa Allah Ya albarkaci zuriyarsu da tsawon rai, domin ita ce babba a cikin ’ya’ya bakwai na mahaifinsu, kuma yawancin kannenta sun kai shekaru fiye da tamanin a duniya kafin su rasu. Ta bayyana sunayen wadanda suka rasu da Malam Muhammadu da Malam Ali da Hajiya Mairiga da kuma ’yar autarsu Malama Zainabu-Abu wacce ta rasu wata biyu da suka wuce. Kuma Hajiya Mairiga da Hajiya Mai-Saro suna nan da ransu a Kano, ita kuma tana zaune a Kaduna a yanzu.
Amina ta ce bayan da ta auri mijinta wanda soja ne da ya je Yakin Duniya na Biyu ya dawo sun zauna a Asibitin 44 na sojoji da ke Kaduna, kuma da Yakin Basasa ya zo ya yi yaki ya kuma horar da kurata. Ta ce mijinta Samanja Muhammadu Ma, Bafulatani ne dan asalin garin Fika da ke Jihar Yobe kuma Allah Ya yi masa rasuwa ne a 1992.
Malama Amina ta ce tana da ’ya’ya hudu da jikoki 42 da tattaba-kunne 90 da inhinhin takwas, jimilla zuriyarta sun kama mutum 144 masu rai.
Ta ce lalurar da Allah Ya dora mata ita ce ta taba zamewa ta fadi ta samu gwocewa kimanin shekara takwas. Ta ce ta gode Allah inda ’ya’ya da jikoki da sauransu ke yi mata hidima ba dare ba rana.
Malama Amina ta ce idan ana bikin aure ko suna ko wani taro to gidanta kan yi kadan sai an shiga gidajen makwabta.
Amina Muhammad ta ce tana cin kowane irin abinci da kowa yake ci, kamar tuwo da teba da miyar kubewa da shayi da burodi kuma tana son kankana.
Wani abin mamaki game da wannan zuriya shi ne akwai dangin dattijuwar da ke zuwa kasuwanci kasar Afirka ta Tsakiya da suka ji dadi suka zauna a can. Wata daga cikin dangin tana zuwa Kano don sarin kaya ta kai Afirka ta Tsakiya ta sayar. Da Allah Ya yi mata gyadar-dogo sai ta tambayi wanda take sarin kaya a wurinsa inda ya gaya mata cewa ai ita danginsa ce. Sai ta ce in ta dawo, za ta samu lokaci ta je ta ga sauran danginta a gida. Kwatsam, tana komawa kasar Afirka ta Tsakiya sai Yakin Basasa ya barke a can, inda ta tattaro danginta, ba ta yada zango ko’ina ba sai wurin wannan dan uwa nata a kasuwa, inda ya zarce da wannan ayari gidansu na gadon-gado a tsakiyar birnin Kano.