Na yi zamani da shugabannin Najeriya 7 a matsayin babban mai daukar hoto – Baba Shettima
Baba Shettima mai hoto a iya cewa shi ne Shugaban kasa na masu hoto a Najeriya, inda ya yi zamani da shugabanni takwas albarkacin wannan sana’a kuma ya samu kasancewa cikin mutum 100 da suka gana da Sarauniyar Ingila lokacin da ta zo Najeriya. Ya shaida wa Aminiya yadda ya faro wannan sana’a tun daga […]
Baba Shettima mai hoto a iya cewa shi ne Shugaban kasa na masu hoto a Najeriya, inda ya yi zamani da shugabanni takwas albarkacin wannan sana’a kuma ya samu kasancewa cikin mutum 100 da suka gana da Sarauniyar Ingila lokacin da ta zo Najeriya. Ya shaida wa Aminiya yadda ya faro wannan sana’a tun daga kwaleji kuma ya kai matsayin da ya yi hira da Sarauniyar Ingila tare da bajen kolin hotuna a kasar nan da Ingila:
Aminiya: Za mu fara da tarihinka?
Baba Shettima: Assalamu alaikum, sunana Yakubu Shettima, amma an fi kira na da Baba Shettima, saboda sunan mahaifina aka sanya min. An haife ni a Potiskum, Jihar Yobe a ranar 1 ga Oktoba, 1946. Na yi karamar firamare da babba a Potiskum, sannan na kammala Kwalejin Barewa a 1960. A Kwalejin Barewa na fara aikin daukar hoto, a makarantar akwai kulob na daukar hoto. Na yi shekarar biyar ina koyon aikin hoto, bayan na kammala, sai na fara aiki a Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar Kaduna, inda na fara daukar hoton wasan gona da aka yi a Zariya.
Ina daya daga cikin masu daukar hoton da suka dauki hotunan ayyukan marigayi Sardauna da Sa Kashim da sauransu, bayan an kirkiro jihohi 12 sai na koma jiharmu ta Arewa maso Gabas, daga nan na samu gurbin karo karatu a wata makarantar koyar da daukar hoto da ake kira Kytsone College of Technology da ke birnin Leeds a Ingila, a nan na shekara biyu.
Bayan na kammala na ci gaba da aiki a Jihar Arewa maso Gabas, daga baya na sake komawa Ingila na sake yin kwas wajen aikin daukar hoto, inda a 1982 na zama Babban Jami’i mai daukar hoto na kasa. Da farko ban damu da tattara hotuna ba, amma bayan da na ga al’amura sun fara tabarbarewa sai na fara tara hotuna don kashin kaina. Haka na rika tara hotunan har na yi ritaya a shekarar 2000. A yanzu kuma ina zaman kaina ne.
Aminiya: Me ya ja hankalinka har ka zabi aikin daukar hoto?
Baba Shettima: Sha’awa ce ta sanya na zabi daukar hoto, a lokacin a makaranta akwai kulob-kulob masu yawa, to, mutum zai zabi daya da kuma fatan gaba wannan abin ya amfane shi. Bari in ba ka misali, a da duk Najeriya ba makarantar da take da yawan sojoji kamar Kwalejin Barewa, hakan ya samu ne saboda akwai cadet a makarantar, da haka suka tashi har son soja ya shiga ransu. Tunda aka kafa makarantar ni ne kadai na yi aikin hoto.
Aminiya: A lokacin su waye abokan karatunka?
Baba Shettima: Akwai Bello Tunau Mafara da Dokta Mohammed Abdurrahman da marigayi Farfesa Ilyasu Mohammed da marigayi Manjo-Janar Ibrahim dahiru Gumel da Mohammed Biodun Sunmonu da Aminu Adisa Logun da sauransu.
Aminiya: Bayan ka zama babban jami’in daukar hoto na kasa, shugabannin kasa nawa ka yi aiki da su, a ciki wanne ka fi jin dadin aiki da shi?
Baba Shettima: Na ji dadin aiki da su, amma na fi jin dadin aiki da marigayi Sardauna duk da cewa a lokacin ban fara aiki a Gwamnatin Tarayya ba. Bayan na dawo Gwamnatin Tarayya sai ya zama duk wani aikin daukar hoto na karkashina, lokaci zuwa lokaci nakan yi aikin daukar hoto a gidan gwamnati, na fara aikin daukar hoto a gidan gwamnati a lokacin Shagari, na ji dadin aiki da shi, haka sauran shugabannin kasa ma, kodayake daga baya abubuwa sun tabarbare, ba kuma yadda muka so ba. Bayan Shagari ya tafi wato lokacin Buhari ke nan, sai ya yanke Ma’aikatar Watsa Labarai daga harkokin gidan Shugaban kasa, sannan ya dauko Babban mai watsa labarai na kasa a lokacin, shi kuma sai ya kawo wani mai daukar hoto dan garinsu Katsina ke nan, mun ji dadin aiki amma ba yadda muke so ba. Da haka har na bar aiki a lokacin Obasanjo na farar hula.
Aminiya: Bayan ka sanar wa iyayenka ka zabi daukar hoto me suka ce?
Baba Shettima: Mahaifina ya rasu ina aji daya a sakandare, ni ne na yi wa kaina zabi.
Aminiya: Wasu matsaloli ka fuskanta a lokacin da kake aikin daukar hoto?
Baba Shettima: A wajen aiki babu matsala, duk abin da nake bukata kama daga hakkina zuwa kayan aiki ina samu.
Aminiya: Batun nasarori fa?
Baba Shettima: Na bude wata makaranta da nake koyar da aikin daukar hoto, inda jihohi sukan turo ma’aikatansu mu koya musu daukar hoto, haka ma sojoji da ’yan sanda da jami’an shige da fice duk suna turo jami’ansu mun koya musu. Ni ne mai daukar hoto a Najeriya kadai da ya yi bikin baje-kolin hotuna a wurare uku, na yi haka ne a lokacin da Najeriya ta yi bikin cika shekara 53 da samun ’yancin kai, na fara a Abuja, sai Gwamnatin Jihar Legas ta gayyaci ne na yi a Legas, sannan ’yan Najeriya da suke Ingila su ma suka gayyace ni. A lokacin bikin an gayyaci Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo. Sannan a bara ma na yi bikin baje-kolin hotuna a Washingon DC da ke Amurka.
Aminiya: Yaya kake daukar hoto a baya?
Baba Shettima: Yadda muke daukar hoto a da ya bambanta da yanzu, a yanzu komai ya zama na zamani, inda ake amfani da kwamfuta. A lokacin baya mai hoto ne zai dauki hotonsa, sannan babu wata na’ura da za ta shirya wa mai daukar hoto komai, shi da kansa zai shirya komai, kama daga hasken da zai shiga kyamara da kuma saurin kyamarar da sauransu, idan ya dauki hoton, sai ya je dakin wankewa, ya wanke dodon hoton, sannan mai hoton da kansa zai wanke hoton, babu sauri, amma akwai dadi, idan ya wanke hoton, sai ya rubuta masa suna da lokaci da kuma wurin da aka dauka, sannan ya kai wurin da ake bukata, wato idan za a buga a jarida ko za a ajiye shi, amma na yanzu komai kyamara za ta yi maka, sannan ka kai gidajen wanke hoto a wanke maka.