Na yi zamani da shugabannin Najriya 7 a matsayin babban mai daukar hoto
Aminiya: Wadanne kayan aiki ka yi amfani da su a lokacin?Baba Shettima: A lokacin na yi amfani da kyamarori masu yawa, amma mai tsadar ita ce Haphazard, ana sayar da ita Naira 600, sai Roli-Fled ana sayar da ita 200 zuwa 300, amma dai kudin yana da daraja, sai Flash Electronic don ba da haske […]
Aminiya: Wadanne kayan aiki ka yi amfani da su a lokacin?
Baba Shettima: A lokacin na yi amfani da kyamarori masu yawa, amma mai tsadar ita ce Haphazard, ana sayar da ita Naira 600, sai Roli-Fled ana sayar da ita 200 zuwa 300, amma dai kudin yana da daraja, sai Flash Electronic don ba da haske da sauransu.
Aminiya: Yaya za ka kwantata wahalar aikin a lokacin?
Baba Shettima: Babu wahala saboda ka riga ka saba, kodayake yanzu da aka kara samun ci gaba za a iya cewa na da akwai wahala, amma a lokacin ba ma ganin wata wahala.
Aminiya: Har yanzu kana daukar hoto?
Baba Shettima: Ina dauka amma na sha’awa, ko idan na so nishadi, wani lokaci nakan dauki ’ya’yana, ko kuma idan wani abokina zai yi wani biki. Ba na shiga rububi in dauki hoto kamar da. Duk da haka ban bar aikin hoton ba, domin na shiga aikin tattara hotuna.
Aminiya: Me ya ja hankalinka ka fara tattara hotunan?
Baba Shettima: Na fara aikin tara hotuna ne tun ina aiki, domin na lura ba a damu da hotunan ba, sai na yi tunanin nan gaba za su iya bacewa, sai na ce kafin in bar aiki barin in yi wa kasa aiki, shi ne na fara tara hotuna, a watan Janairu zan cika shekara 50 ina aikin daukar hoto. Kowa da yadda Allah Ya jarrabe shi, wani ya tara kudi, to, ni Allah Ya jarrabe ni da daukar hoto da kuma tarawa. Da zarar na ji labarin tsohon hoto, to ko’ina yake zan nemo shi.
Aminiya: Haka na nufin ka yi tafiya mai nisa wajen neman hoto ke nan?
Baba Shettima: A lokacin da nake Legas na je Kaduna da Abuja har zuwa Yola neman tsohon hoto. Akwai wani hoton tarihi na mai, a kansa na bar Legas na zo Abuja, a hoton Firayi Minista Sa Abubakar Tafawa balewa yana kan jirgin da ya fara dakon gurbataccen mai na Najeriya na farko don a tace shi, saboda in san abin da ake ciki, sai na samu Maitama Sule, dan Masanin Kano, ka san ya yi Ministan Ma’adanai da Albakatun kasa, shi ya ba ni labarin komai a kan hoton.
Aminiya: Ka dauki hotuna da yawa ciki har da gidajen sarauta, yaya alakarka take da gidajen sarauta idan ka je aiki?
Baba Shettima: Ina da alaka mai kyau da su, kada ka manta ko an gayyace ka, ko kuma ka nemi a ba ka izini ka dauki hotuna, ko ma wane ne an san da zuwanka, don haka babu wata matsala, kafin ma ka je an san kana zuwa, idan ka je sai ka ga an ba ka martabar da ta kamata. Na tuna lokacin da na je daukar hoton Sarkin Ilorin, Sulu Gambari, tun kafin in je sai na sanar da ofishinmu na Ilorin, su ne suka sanar a fada, tun kafin in je aka shirya komai, fada ce ma ta shirya min masauki da abinci da komai.
Aminiya: Wani abu ne da an ambaci hoto za ka ji ya darsu a ranka?
Baba Shettima: Idan an ambaci hoto, babu abin da yake zuwa min kamar hoton marigayi Sardauna da na dauka na karshe, na dauki hoton ne a lokacin da aka shirya tarbarsa a lokacin da zai dawo daga Saudiyya bayan ya je Umara, yawanci yakan zo ta jirgin sama ne, wato a lokacin ina Kaduna ke nan, bayan mun je filin jirgi sai aka ce ba zai zo da jirgi ba, ashe har ya taho da mota, shi ne na je gidansa da yamma, a lokacin yana zaune shi da mukarrabansa, muka shiga na dauki hotonsu, ba na mantawa da wannan hoton. Hoton shi ne na biyun karshe da marigayi Sardauna ya dauka, na karshe shi ne wanda maigidana wani Bature mai suna Mista Francis Yheur ya dauka, ya dauki hoton ne a lokacin Akintola ya zo sanar da shi halin da ake ciki ana gobe za a yi juyin mulki. Ina tsammanin ya dauki hoton gawar Sardauna lokacin da aka kashe shi, a lokacin da aka kashe su Sardauna mun je gidansa, amma muna tsoro sai muka tsaya a gefen hanya, Mista Yheur ne ya shiga ya dauki hoto, amma bai bar ni na gani ba, domin da kansa ya wanke hoton, kafin lokacin idan ya dauki hoto mu muke wanke masa, amma a wannan lokacin da kansa ya wanke, hakan ya sanya na yi tsammanin ya dauki hoton gawar Sardauna, domin ya hana ni ganin hoton.
Aminiya: Wane ne Mista Yheur?
Baba Shettima: Bature ne da ya yi aiki da Gwamnatin Tarayya, ya shigo Najeriya a 1943, bayan an samu ’yancin kai sai Sardauna ya ci gaba da aiki da shi, bayan na fara aiki da Gwamnatin Tarayya sai Allah Ya hada jinina da nasa, ya rika jana a jiki saboda ya ga ina da sha’awar aikin, akwai lokacin da ake yaki har na yanke shawarar in shiga aikin soja, amma ya hana ni, ya ce in yi hakuri wata rana zan zama wani abu, yanzu ya rasu.
Aminiya: Wane abu na farin ciki ya faru da kai a dalilin daukar hoto?
Baba Shettima: Abin farin ciki da ya faru da ni a dalilin daukar hoto shi ne haduwa ta da Sarauniyar Ingila, ba na je daukar hoto Ingila ba ne, amma dalilin aikin hoto ne. Duk duniya ina tsammanin babu mai aikin hoto da ya dauki hoto da Sarauniyar Ingila sai ni kadai. Ka tuna duk inda Sarauniya ta je ana kawar da masu daukar hoto gefe. Abin da ya faru shi ne, a lokacin Sarauniya za ta kawo ziyara Najeriya a shekarar 2003, sai ofishin jakadancin Ingila a Najeriya, suka rika neman yadda za su faranta mata rai, sai suka nemi hotunan zuwanta Najeriya a 1956, suka je Legas neman hoton amma ba su samu ba, can sai wani ya ce musu su neme ni, sai suka tuntube ni, aka ci sa’a ina da hotunan, suna so, na wanke guda 10 zuwa 15. Na baza hotunan, saboda da jin dadin hotunan bayan an shirya liyafa da Sarauniya, inda aka gayyaci mutane dari sai aka sa da ni, hakan ya sanya ni farin ciki. A lokacin da ake kiran mutane ni ne na hudu, bayan an kira Mai shari’a Uwais da TY danjuma da Jakadan Ingila a Najeriya, sai aka kira ni, muka gaisa da ita. Ta ce mini ta ji dadin ganin hotunan, suna da kyau, ta tambaye ni a ina na yi karatu, na fada mata, da yadda nake daukar hotuna da sauransu. Na fada mata ni mamba ne a kungiyar masu daukar hoto ta Ingila, ni kadai ne mamba daga Najeriya, kuma ke ce uwar kungiyar. Albarkacin daukar hoto na yi hira da Sarauniya.
Aminiya: Ko kana da shawara ga masu daukar hoto na yanzu?
Baba Shettima: Shawarar da zan ba su ita ce, su rike aiki tsakani da Allah. Da yawa suna shiga aikin daukar hoto ne saboda ba su da wani aiki, don haka kafin su fara aikin su tabbatar suna da sha’awarsa, don yanzu kamar ni ba don sha’awa ba da na yi wani aiki. Bayan sha’awa su nemi kayan aikin da suka dace, sannan su rika neman ilimi a kan aikin don tafiya da zamani.