Na zana motoci da yawa – Bashir Aliyu

Gwamnatin Jihar Sakwato a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta dauki nauyin Bashir Aliyu don yin karatun zanen motoci a kasar Amurka. Bashir Aliyu wani matashi ne dan asalin Jihar Sakkwato da ya ce ya zana motoci iri daban-daban har 800 da ka. Bayan ganawar da matashin ya yi da Gwamna Tambuwal, Aminiya ta […]

Na zana motoci da yawa – Bashir Aliyu
Na zana motoci da yawa – Bashir Aliyu

Gwamnatin Jihar Sakwato a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta dauki nauyin Bashir Aliyu don yin karatun zanen motoci a kasar Amurka. Bashir Aliyu wani matashi ne dan asalin Jihar Sakkwato da ya ce ya zana motoci iri daban-daban har 800 da ka.
Bayan ganawar da matashin ya yi da Gwamna Tambuwal, Aminiya ta garzaya gidansu don jin hikimar da Allah Ya ba shi wadda ta sanya gwamnati daukar nauyin karatunsa.
“A takaice dai ni dan Jihar Sakwato ne, na yi karatun firamare da sakandare duk a nan. Tun ina karami nake sha’awar zanen motoci, amma ban fara zanawa ba sai a shekarar 2007. Na fahimci kwakwalwata na dauke da zane sai na zana wata mota da nufin in kera ta in shiga cikinta. Zuwa yanzu dai burina bai cika ba, sai na ajiye ta gefe na cigaba da yin zane-zanen inda nake da zanen motoci 800 a halin yanzu da nake magana da kai suna kan takarda da wasu kadan da na kera da kwalin suturobut,” inji Bashir.
Ya ci gaba da cewa abin da ya kara masa kwarin guiwa bai fi haduwarsa da fitaccen mai zana motoci nan ba Jelani Aliyu na kamfanin General Motors da ke Amurka.
“Na hadu da Jelani a shekarar 2012 a lokacin da ya samu lambar yabo ta kasa, sai Gwamna Wamakko a lokacin ya shirya masa walimar girmamawa a nan na samu labarin ya shigo Sakkwato sai na tafi gidansu na samu kanensa Hussaini na gaya masa abin da ke tafe da ni, na bukatar ganin yayansa. Sai ya ce min mu tafi wurin bikin a can ne zai hada ni da shi, bayan mun tafi ne ya je ya yi masa bayani ga wani yaro da ke zane kamarsa.  Ya ce a kara ni na zo na nuna masa abin da nake yi, ya yaba sosai daga nan muka rika hulda da shi har wannan lokaci,” inji Bashir.
Da ya juya kan yadda aka yi gwamnatin jihar ta san da shi, sai ya ce ta sanadin Jelani wata rana da ya zo Sakkwato sai ya karbi wata mota ja da ya zana sai ya je ya nuna wa Gwamna ga wani yaro da ke yin zane irin nasa, bayan ya yi masa bayani ne ya kuma gaya masa ina bukatar a taimaka min in karo karatu a kasar Amurka kan darasin zana motoci (auto mobile desing) a lokacin suka tattauna maganar har zuwa yanzu da Gwamna ya neme shi tare da alkawarin daukar nauyin karatunsa.
Da ya juya kan kudirin da yake da shi, ya ce ba ya da wani buri da ya fi ya koyo wannan sana’a ya zo ya amfani kasarsa da al’umma gaba daya duk da babu kamfanin mota a nan.  “Ba wai sai na ga mota nake zana tawa ba, hasali ma ban san irin motar da zan zana ba, in na dauki takarda da biro sai bayan na kare zanen ne duk wanda ya gani sai ya yaba ya ce na zana mota mai kyau. Nakan sanya musu sunaye iri-iri yadda nake so kamar Sauka Lafiya da makamantansu,” inji shi.
Bashir Aliyu ya yi fatan duk wani matashi mai basira zai daina wasa da baiwarsa ya tsaya ya taimaki kansa da jama’a. Ya ce duk da ya fuskanci matsaloli da dama a rayuwa amma ga shi bukatarsa na kokarin biya sakamakon jajircewa da nacin da ya sanya a gaba.