NABTEB ta saki sakamakon jarrabawar NBC/NTC na 2022

Kashi 69.6% na wadanda suka rubuta jarrabawar sun samu makin ‘Credit’ a darussa akalla biyar, ciki har da Ingilishi da Lissafi.

NABTEB ta saki sakamakon jarrabawar NBC/NTC na 2022

Hukumar shirya jarrabawa ta NABTEB, ta saki sakamakon jarrabawar NBC da NTC na 2022 da aka rubuta.

Shugabar hukumar, Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe ce ta sanar da hakan yayin taron manema labarai da suka shirya ranar Laraba a Benin.

Da take jawabi ta bakin wakilinta kuma darakta a hukumar, Dokta Obinna Opara, ta ce mutum 87,668 ne suka rubuta jarrabawar a cibiyoyi 1,656 a fadin Najeriya da kasar Kwaddibuwa.

Farfesa Isiugo-Abanihe ta ce, lura da jimillar wadanda suka rubuta jarrabawar, an samu kari a yawan wadanda suka rubuta jarrabawar a 2021 da kashi 4.99 cikin 100.

Ta kara da cewa, mutum 58,569 (kashi 69.6 cikin 100) daga cikin wadanda suka rubuta jarrabawar sun samu makin ‘Credit’ darussa a akalla biyar, ciki har da Ingilishi da Lissafi.

Ta bayyana cewa duk da haka, kokarin da dalibai suka nuna a jarrabawar bara ya zarce na bana idan aka yi la’akari da yanayin darajar makin da suka samu.