Nada Aisha minista ya jawo takaddama tsakanin APC da PDP a Sakkwato

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Sakkwato Alhaji Suleman danmadamin Isa ya bayyana cewa sun juya wa wadda shugaba Buhari ya nada a matsayin minista mai wakiltar jihar Sakkwato baya ne saboda ba ’yar jam’iyyar APC ba ce kuma babu wanda ya santa. Ya yi wannan bayanin ne a yayin da yake wa manema labarai bayani […]

Nada Aisha minista ya jawo takaddama tsakanin APC da PDP a Sakkwato
Nada Aisha minista ya jawo takaddama tsakanin APC da PDP a Sakkwato

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Sakkwato Alhaji Suleman danmadamin Isa ya bayyana cewa sun juya wa wadda shugaba Buhari ya nada a matsayin minista mai wakiltar jihar Sakkwato baya ne saboda ba ’yar jam’iyyar APC ba ce kuma babu wanda ya santa.

Ya yi wannan bayanin ne a yayin da yake wa manema labarai bayani bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyarsu, inda duk wani mai mukamin jam’iyya da na siyasa suka hallara.
Ya ci gaba da cewa,“Mun kira taro ne don mu sanar wa jama’armu abin da ke faruwa a kasar nan, musamman kan nada muna wata Aisha Abubakar a matsayin minista mai wakiltar Sakkwato, ba ’yar jam’iyya ba ce, ko kiranta ka yi ba za ta iya gaya maka sunayen shugabanin mata na jam’iyyarmu ba, muna son a musanya ta da wadanda da suka cancanta ‘yan jam’iyya da suka sadaukar da kansu don samun nasaara a zaben da ya gabata.”
danmadami ya kara da cewa, “dukanmu tun daga kan gwamna mun yarda mu rubuta wa Mai girma Shugaban kasa takarda neman sauyi na wannan matar, don ta fito gari daya da Gwamnan jiha Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, kuma babu wanda ya santa ko ta sani a siyasance.’’
Shi ma Alhaji Kabiru Aliyu, Sakataren Jam’iyar PDP a jihar Sakkwato, ya yi wa Aminiya bayani kan Ministar, inda ya ce, “Mun tsaya da idon basira mun kalli wadannan abubuwan hauragiya da APC ke yi, dalili kuwa shi ne, hujjarsu ta rashin aminta da ita shirme ne da babu da makama. Sun fadi cewa ita ba ’yar APC ba ce, to ina aka ce ba a nada minista sai ’yar jam’iyya? tarihi ya nuna ana nada minista ga wanda ba ya kasar, kamar Ngozi da sauransu.”
Ya kara da cewa, maganar ta fito yanki daya da gwamna, a can baya lokacin gwamnatin Wamakko yana gwamna Barista Inuwa da Dakta Haliru da Ahmad Gusau duk yankinsu daya da gwamna kuma kowanensu ya yi minista, maganar ba ta cancanta ba, maganar banza ce, don ba a taba minista wadda take da gogewa ba irinta, ta hanyar ilmi da wayewa, don ta mallaki digiri na biyu wanda dukkan minitocin da muka yi digirin farko ne suke da shi, ta kware wajen sanin tattalin ariziki, wanda wannan gwamnatin ke bukata kuma ta sanya a gaba, don haka tana bukatar shawarwarin wadannan masana irin su Aisha. Kalaman cewa ba ta cancanta ba maganar banza suke yi, su daina kallonta a matsayin wata da ke da alaka da PDP don danginta na jam’iyyar.