Nada mukamin Karamin Minista ya saba wa tsarin mulki — Keyamo
Karamin Minista ba shi da wani iko na a zo a gani.
Karamin Ministan Kwadago da Ayyuka mai barin-gado, Festus Keyamo (SAN), ya gaya wa Shugaba Muhammadu Buhari mai barin-gado cewa nada mukamin Karamin Ministan ya saba wa tsarin mulkin kasar.
Keyamo wanda babban lauya ne a Najeriya ya fadi hakan ne a jiya Laraba, lokacin da yake gabatar da jawabinsa a zaman majalisar zartarwa na ban-kwana domin kawo karshen majalisar, wanda Shugaba Buhari ya jagoranta a Abuja.
- Yau ake fara bukukuwan mika mulki ga sabuwar gwamnati
- Jajibirin mika mulki: Buhari na neman biyan bashin N539bn na aikin shari’a
Karamin ministan ya nuna cewa wannan mukami da ake bai wa mutane yawanci da sunan gwamnatin hadin kan kasa kusan ba ya aiki a zahiri ga yawancin wadanda ake nadawa a matsayin.
Domin ba wani iko na a-zo-a-gani da suke da shi, lamarin da a wani lokacin ma yake hada su rigima da wanda yake matsayin ainihin matsayin ministan.
Ya ce yawancin wadanda gwamnatocin baya suke nadawa a wannan mukami sun ki fitowa su yi magana ne saboda kar a ga ba su gode wa shugabannin kasar da suka ba su mukamin ba.
Festus Keyamo shi ne kakakin rusasshen kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu da Shettima.