Nadal zai yi ritaya daga Tennis

Nadal ya ce al’amura sun yi tsanani a ‘yan shekarun baya-bayan nan, musamman ma shekaru biyu da suka gabata.

Nadal zai yi ritaya daga Tennis

Fitaccen ɗan wasan tennis, Rafael Nadal, ya bayyana cewa zai yi ritaya daga wasan a ƙarshen kakar bana.

Nadal wanda ɗan ƙasar Spain ne zai yi ritaya a matsayin ɗaya daga cikin zaratan wasan tennis wanda kawo yanzu ya samu nasarar lashe babban kofin wasan tennis wato grand slam guda 22.

“Zan yi ritaya daga wasan kwallon Tennis. A zahiri al’amura sun yi tsanani a ‘yan shekarun baya-bayan nan, musamman ma shekaru biyu da suka gabata,” inji Nadal a cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.

“Hakika wannan shawara ce mai wahalar yankewa, wacce ke ɗaukar tsawon lokaci kafin a yanke, sai dai a rayuwa duk abin da ya yi farko ta zai yi karshe.”

Nadal mai shekaru 38 wanda ya fara wasan tennis a matakin ƙwararru a shekarar 2001 ya lashe gasar grand slam a shekarar 2005 ne, inda ya doke ɗan wasan Argentina, Mariano Peurta a wasan ƙarshe na French Open.

Ya lashe gasar ce a karon farko da ya fafata, inda ya zama ɗan wasa na biyu da ya lashe gasar a fafatawar farko.

Nadal ya samu mutunci a idon duniya tare da zama gwarzon da ake koyi da shi, da kuma yin gogayya da zaratan ‘yan wasan tennis irin su Roger Federer da Novak Djokovic.

A shekarar 2022 ce ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan Tennis, Roger Federer ya yi tasa ritayar daga buga wasan Tennis yana da shekaru 41 a duniya.

Federer ya yi wasansa na ƙarshe a gasar Laver Cup da ta gudana a Landan, inda shi da abokin hamayyarsa Rafael Nadal suka buga wasan mutum biyu-biyu da Frances Tiafoe da Jack Sock.

Dan asalin kasar Switzerland din na hawaye a lokacin da yi jawabinsa na karshe ga masu kallon da suka cika filin wasan domin yin bankwanan ƙarshe ga gwaninsu.

A shekarar 2021 ce a yayin gasar Wimbledon, fitaccen dan wasan ya fice daga gasar bayan da Hubert Hurkacz ya doke shi a zagayen kusa da na ƙarshe, kafin nan, ya sha fama da ciwon gwiwa da ya hana shi sukunin buga ƙwallon.

Shi ma dai Federer ya lashe gasar Grand Slam sau 22 a tarihi kuma ya buga wasanni sama da 1,500 a cikin tsawon shekaru 24.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya