Nade-nade: Jonathan ya kori Shugabar Asusun Man Fetur
A ci gaba da kora da nade-nade da Shugaba Goodluck Jonathan ke yi a daf da karshen wa’adin mulkinsa, a ranar Talata Jonathan ya kori Shugabar Asusun Daidaita Farashin Man Fetur (PEF) Misis Sharon Adefunke Kasali tare da nada Minista a Ma’aikatar Gona Misis Asabe Asma’u Ahmed a madadinta, kamar yadda wata sanarwa daga Kakakin […]
A ci gaba da kora da nade-nade da Shugaba Goodluck Jonathan ke yi a daf da karshen wa’adin mulkinsa, a ranar Talata Jonathan ya kori Shugabar Asusun Daidaita Farashin Man Fetur (PEF) Misis Sharon Adefunke Kasali tare da nada Minista a Ma’aikatar Gona Misis Asabe Asma’u Ahmed a madadinta, kamar yadda wata sanarwa daga Kakakin Shugaban kasa Rueben Abati ce ta bayyana.
Misis Asabe Ahmed, ta maye gurbin Sharon Kasali ce wadda take shugabancin asusun na PEF tun shekarar 2007.
Sabuwar Babbar Sakatariyar Asusun na PEF ta fito ne daga Jihar Neja, kuma tana da Digiri na daya da na Biyu daga Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya da Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Soja (NDA) da ke Kaduna.
Har wa yau Shugaba Jonathan ya amince da nada Mista Denzil Amagbe Kentebe a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Yankuna ta Najeriya, (NCDMB).
Mista Kentebe, wanda masanin zayyane-zayyane ne ya maye gurbin Mista Ernest Nwapa wanda yake kan kujerar tun watan Afrilun shekarar 2010.
Sauran nade-naden da Shugaban mai barin gado ya yi sun hada da nada tsohuwar Ministar Tsaro, Olushola Obada da tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel a mtsayin shugabannin hukumomin gudanarwa na Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma da Jami’ar Tarayya da ke Kashere.
Tuni Jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas ta soki nade-naden da Shugaban ke yi a karshen mulkinsa inda ta ce wani tarko yake kafa wa gwamnati mai zuwa ta Janar Muhammadu Buhari, ta yadda idan Buhari ya sauke su, zai rasa goyon baya daga jama’a kamar yadda shugaban jam’iyyar Dokta Dabies Ibiamu Ikanya ya bayyana a wata sanarwa.