Nadin Hakeem Baba-Ahmed ya nuna Tinubu ya shirya yin aiki
Dattawan Arewa sun bukaci Hakeem Baba-Ahmed ya ba wa Tinubu shawarwari na gari domin ci gaban Najeriya

Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Hakeem Baba-Ahmed
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce nadin da Shugaba Tinubu ya yi wa kakakinta, Dokta Hakeem Baba-Ahmed a matsayin hadimin mataimakin shugaban kasa ya nuna shugaban ya shirya samar da romonn dimokuradiyya ga al’ummar Najeriya.
Darakta-Janar na kungiyar NEF, Farfesa Doknan Sheni, ya sanar a ranar Talata cewa nadin Hakeem Baba-Ahmed kwakkwarar alama ce ta Gwamnatin Tinubu ta shirya cin moriyar irin hikima da basira da Allah Ya ba wa ’yan Najeriya daga bangarori daban-daban.
- Yau kotu za ta yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano
- DAGA LARABA: Matakan Nasara Wajen Neman Aure A Soshiyal Midiya
“Muna fata Shguaban Kasa zai yi cikakken amfani da basirar Dokta Hakeem Baba-Ahmed wajen gudanar da gwamnati domin cigaban kasa baki daya,” in ji shi.
Farfesa Sheni ya kuma yi kira ga Dokta Baba-Ahmed da sauran wadanda aka nada a mukamai da su ba wa Shugaba Tinubu nagartattun shawarwari domin magance matsalolin dake ci wa Najeriya tuwo a kwarya.