Nadin sabon Sarkin Misau ya ta da kura
Nadin tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi Alhaji Ahmed Suleiman a matsayin sabon Sarkin Misau da gwamnatin jihar ta yi, ya ta da kura inda rahotannin suka ce wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga tare da kone wani bangare na fadar Sarkin Misau din da kuma wasu motoci, inda suka bazama kan tituna suna ta lalata […]
Nadin tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi Alhaji Ahmed Suleiman a matsayin sabon Sarkin Misau da gwamnatin jihar ta yi, ya ta da kura inda rahotannin suka ce wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga tare da kone wani bangare na fadar Sarkin Misau din da kuma wasu motoci, inda suka bazama kan tituna suna ta lalata dukiyoyin jama’a.
Gidan rediyon BBC da wasu kafafen watsa labarai da suka ruwaito labarin sun ce an baza jami’an tsaro a garin, wadanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen kwantar da tarzomar.
A jiya Alhamis ne wata sanarwa dauke da sanya hannun Babban Sakatare mai kula da Harkokin Siyasa a Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi, Malam Hashimu Yakubu da aka raba wa manema labarai ta bayyana nadin Alhaji Ahmed Suleiman. Takardar ta ce: “Sakamakon rasuwar Sarkin Misau na 10, Alhaji Muhammadu Manga III a ranar Litinin 17 ga Agusta, bisa ikon da sashi na 3 (i) na dokar nadi da sauke sarakuna, Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Mohammed Abubakar, ya amince da nadin Alhaji Ahmed Suleiman a matsayin Sarkin Misau na 11.”
Sai dai wannan nadin ga alama bai yi wa wasu jama’ar masarautar dadi ba, domin ana bayyana nadin garin Misau fadar masarautar ya fara tajin-tajin, inda wasu suka yi zargin an sanya siyasa a cikin batun.
Wata majiya ta ce matasa sun kone motoci uku da ke cikin ayarin sabon Sarkin, sannan sun tare hanyoyin garin don nuna bacin ransu.
Wata majiyar masarautar ta ce an ga hayaki yana tashi a fadar Sarkin Misau amma ba ta san hakikanin irin barnar da ta shafi fadar ba.
An tura karin jami’an tsaro garin Misau inda suka yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa matasan, sai dai har zuwa rubuta wannan rahoto Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ba ta fitar da wani bayani kan batun ba.
Masarautar Misau daya ne daga cikin masarautun Bauchi masu daraja ta daya, kuma masarauta ce da take da tutar Mujaddadi Shehu Usman dan Fodiyo.