Nadin Sanusi falala ne ga Kanawa – Kwankwaso
Gwamnan Jihar Kano, Injinia Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce nadin Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II falala ce ga Kanawa, inda ya ce lura da iliminsa na addini da gogewa yana da yakinin zai kawo gagarumin sauyi a Kano.Wata sanarwa dauke da sanya hannun Daraktan Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamnan, […]

Gwamnan Jihar Kano, Injinia Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce nadin Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II falala ce ga Kanawa, inda ya ce lura da iliminsa na addini da gogewa yana da yakinin zai kawo gagarumin sauyi a Kano.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Daraktan Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamnan, Malam Halilu Ibrahim dantiye, ta ce Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar tsohon Sarkin Gwandu, Alhaji Mustapha Haruna Rashid, wanda ya ziyarci jihar domin ta’aziyya ga jama’arta dangane da rasuwar marigayi Sarkin Kano Ado Bayero tare da taya sabon Sarki, Alhaji Muhammadu Sanusi na II murnar nada shi.
“Nadin Muhammadu Sanusi na II zai kasance falala ga al’ummar jihar, idan aka lura da ilimi da kwarewarsa. Kuma ina fata jama’a za su hada kai da shi domin ya samu damar yi musu hidima yadda ya kamata,” inji Gwamnan.
Gwamna Kwankwaso ya kara da cewa, gwamnatinsa ta sadaukar da kai wajen zaba wa al’ummar jihar abin da ya fi dacewa a kowane fanni na rayuwa, inda ya ce wannan ne abin da ake fata ga shugaba ya yi wa jama’arsa, domin yin sabanin hakan ba zai zame alheri ba.
Gwamnan ya gode wa tsohon Sarkin Gwandun kan yi wa al’ummar Kano ta’aziyya da kuma yin kalaman karfafa gwiwa kan sauye-sauyen raya kasa da ake samu a jihar.
Tunda farko Alhaji Mustapha Haruna Rashid ya ce marigayi Sarki Ado Bayero ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban Musulunci ba a jihar kadai ba har a sassan kasar nan, inda ya roki Allah Ya saka masa da Aljanna.
Sai ya yaba wa Gwawmna Kwankwaso kan zabo magajin da ya dace ga marigayi Ado Bayero da yadda ya tafiyar da hatsaniyar da ta taso bayan an bayyana sunan sabon Sarkin, inda ya ce an sha samun irin wannan tarzoma a baya a wurare da dama. Ya ce, a 1915 sai da aka shafe kwana 40 ana tarzoma lokacin da aka nada daya daga kakanninsa a matsayin Sarkin Gwandu.
Ya yi magana sosai kan sauye-sauyen da ake samu a jihar inda ya yi kira ga gwamnonin Najeriya su yi koyi da hangen nesan Gwamna Kwankwaso domin bunkasa kasar nan musamman a bangaren ilimi.