NAF ta hallaka Boko Haram 32 a Borno
An sake tura ƙarin dakaru zuwa yankin domin tabbatar da tsaro.
Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta kashe ’yan ta’addan Boko Haram 32, a wani farmaki da ta kai garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno.
Rahoton ya bayyana cewa farmakin ya auku ne a ranar 18 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 10:15 na safe.
- Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina
- Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato
Wannan na zuwa ne bayan ’yan ta’addan sun kai hari hedikwatar ’yan sanda da ke Banki.
A lokacin kai farmaki , sojoji biyu sun rasa rayukansu, haka kuma wani ƙaramin yaro mai shekara tara, Ismail Abubakar, ya rasu.
Har ila yau, maharan sun ƙone motocin soja uku.
Bayan kai harin, sojin sama na Operation Had6in Kai sun tura jirgin A-29 Super Tucano wanda ya yi wa ’yan ta’addan ruwan wuta.
Wannan ya janyo mahara 32 sun mutu sakamakon ɓarin wuta da suka sha.
An kwashe gawar sojojin zuwa Maiduguri, yayin da aka miƙa wa iyayen yaron gawarsa domin yi masa sutura.
Daga ƙarshe, an ƙara tura jami’an tsaro zuwa Banki domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.