NAF ta hallaka ’yan ta’adda sama da 70 a Borno
Dakarun sun jadadda aniyar ci gaba da yaƙar ‘yan ta’adda a faɗin Najeriya.
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kashe ’yan ta’adda sama da 70 a hare-haren sama da ta kai tsibiran Kwallaram da Arainna a Jihar Borno.
A cewar Manjo Janar Edward Buba, an kashe wasu ’yan ta’adda da dama a hare-haren, kuma sojoji sun ƙara kaimi wajen yaƙar su a faɗin Najeriya.
- An naɗa ni minista don ƙwato wa APC Kano — Ata
- Tinubu zai halarci taron ƙasashen Larabawa da Musulunci a Saudiyya
“Sojoji za su ci gaba da kai hare-hare don kawar da duk wata barazana,” in ji Manjo Janar Buba.
Ya ce dakarun sun samu nasarar wargaza sansaninsu a wurare da dama.
A cikin wasu hare-haren da sojojin suka kai a baya-bayan nan, sun kashe ‘yan ta’adda 169, sun kama wasu 641, sannan sun ceto mutum 181 da aka sace.
Hakazalika, sun kuma ƙwace ɗaruruwan makamai, dubban harsasai, tare da lalata wasu wurare a yankin Neja Delta.
Sojojin sun karya lagon ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, wanda haka ya sa suka neman sabbin mabiya a shafukan sada zumunta.
Sojojin Najeriya sun sha alwashin kawar da duk wara barazanar ’yan ta’adda.
Buba, ya ce ruwan wutar da suka yi a baya-bayan ya tilasta wa ’yan ta’adda, musamman ƙungiyar ISWAP, fara ƙoƙarin ɗaukar matasa ta hanyar amfani da shafukan sada zumunta.
Har ila yau, ya ce ayyukan sojojin na da nufin karya lagon ƙungiyoyin ’yan ta’adda tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin da ma Najeriya baki ɗaya.