NAFDAC ta ƙona kayayyakin jabu da suka kai na Naira biliyan 1.3 a Abuja
NAFDAC ta ƙona kayyakin jabu da wa’adin aikinsu ya ƙare da kuma marasa inganci da darajarsu ta kai kuɗi Naira biliyan ₦1.3bn a Abuja.
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta ƙona kayayyakin abinci na jabu da wasu suka miƙa ga hukumar daga ƙungiyoyi na cikin gida da na ƙasa da ƙasa da suka haɗa da: Hukumar samar da abinci ta duniya WFP.
Hukumar NAFDAC ta ƙona kayayyakin jabu da wa’adin aikinsu ya ƙare da kuma marasa inganci da darajarsu ta kai kuɗi Naira biliyan ₦1.3bn a Abuja.
- Mun gaji da cewa Najeriya na da damarmaki – Minista
- Gobara ta ƙone shaguna da kadarori a kasuwar Edo
Darakta Janar na Hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, wanda Festus Ukadike ya wakilta, wanda ya jagoranci jami’an hukumar zuwa wurin zubar da shara na garin Kuje a Abuja, ya ce kayayyakin da aka ƙona sun haɗa da ƙwayoyin magunguna, kayan aikin asibiti, kayan kwalliya, kayan abinci da dai sauransu.
Ya kuma ƙona kayayyakin abinci da wa’adin amfani da su ya ƙare daga wasu ƙungiyoyi na cikin gida da na ƙasa da ƙasa, ciki har da hukumar samar da abinci ta duniya WFP suka miƙa.