NAFDAC ta cafke ‘Baban Aisha’ mai maganin gargajiya
An kama shi ne bisa sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba
Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama fitaccen mai harhada magungunan gargajiyar nan, Alhaji Salisu Sani, wanda aka fi sani da Baban A’isha.
An kama shi ne bisa zargin harhada magungunan gargajiya da lasisin da ya tashi aiki.
Da take jawabi ga manema labarai a Abuja, Shugabar Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan, inda ta kuma ce an kama shi ne saboda talla da kuma sayar da magungunan ba bisa ka’ida ba.
Ta ce a kwanan ne hukumae ta yi nazari a kan wani rahoton korafi da wata kafar yada labarai ta wallafa a kan magungunan da Baban A’ishar ke sarrafawa.
Farfesa Adeyeye ta ce rabon da Baban A’isha ya sabunta lasisin nasa tun a shekara ta 2020 saboda bai cika ka’ida ba, alhalin ya kare tun a shekara ta 2018.
Ta ce sakamakon yawan korafe-korafen da ake yi a kafafen sada zumunta na zamani, sashen bincike da tabbatar da bin doka na hukumar ya yi nazari tare da daukae matakin da ya kai ga rufe kamfanin da ake sarrafa maganin da kuma kama biyu daga cikin ma’aikatansa.
Shugabar ta NAFDAC ta ce sun fara aikin binciko masu sarrafawa tare da sayar da jabun magungunan gargajiya a sassan Najeriya daban-daban.