NAFDAC ta gano wani jabun maganin malaria da ke yawo a Najeriya

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya NAFDAC ta yi gargaɗin cewa akwai wani jabun maganin malaria da ke yawo a cikin ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da NAFDAC ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis. Kotu za ta karɓi shaidar wakilin Aminiya a shari’ar garkuwa da mutane An daƙile […]

NAFDAC ta gano wani jabun maganin malaria da ke yawo a Najeriya

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya NAFDAC ta yi gargaɗin cewa akwai wani jabun maganin malaria da ke yawo a cikin ƙasar.

Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da NAFDAC ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis.

Hukumar ta yi bayanin cewa wani kamfani daga Indiya ne mai suna Strides Arcolab Limited ne ya samar da maganin mai suna Combiart.

“An gano maganin na jabu ne a Babban Birnin Tarayya Abuja da Jihar Ribas yayin aikin sa ido na jami’an mu,” in ji sanarwar NAFDAC.

Ta ce binciken da suka yi a ɗakin gwaje-gwaje a kan maganin ya nuna cewa ba shi da inganci sannan akwai kura-kurai kan yadda aka rubuta a jikin kwalin maganin na jabu.

Hukumar ta ce maganin ya daina aiki kuma lambar rijistar NAFDAC da ke jikinsa ita ma ta bogi ce.

Dangane da hakan ne NAFDAC ta yi gargaɗin cewa jabun maganin na da illa ga lafiyar ɗan Adam, la’akari da cewa ba shi da ingancin da ya kamata.