NAFDAC ta gurfanar da masu sayar da jabun magunguna a Kano
Waɗannan magunguna ba sa ƙunshe da sinadaran haɗa magani ko kadan.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta gurfanar da wasu mutane uku tare da wani kamfani a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano bisa zarginsu da hadawa tare da sayar da magunguna na jabu da marasa inganci a jihar.
Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta ce ana tuhumar mutanen Amao Gideon da Alumona Godwin Okwiludili da kuma Hillary Onah Paul Chigozie da Kamfanin Giddyson Healthcare Limited, da laifuka biyar, “bayan kama su da laifin samar da magunguna marasa kyau da babu ingantattun sinadarai a cikinsu.”
Lauyan masu kara, Barista Oche M. Abutu ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin sun hada kai suna sana’a da tare da rarraba da kuma sayar da magungunan jabu masu yawa wanda yawancinsu na yara ne.
- Ƙiba ta kashe birin da ake ciyar da shi kayan daɗi
- Sirrin da Real Madrid ke rawar gaban hantsi a Gasar Zakarun Turai
“Magungunan sun hada da Asian Ampicillin 125mg + Cloxacillin 125mg/5ml – Zero active ingredients. Asian Ampicillin 125 mg/Sml Zero active ingredient Erythromycin 125 mg/5ml – Zero active ingredient Artil-Go (Artemether 20 mg+ Lumefantrine1 20 mg/5ml)-Zero active ingredient.”
Mista Abutu ya ƙara da cewa gwaje-gwajen da aka yi a ofishinta na Kaduna sun nuna cewa waɗannan magunguna ba sa ƙunshe da sinadaran haɗa magani ko kadan, “wanda hakan ke jawo mummunar barazana ga lafiya da ma jawo haɗarin mutuwa.”
Sai dai lokacin da aka karanta musu takardar karar dukkanninsu sun musanta aikata laifuka da suka hada da hadawa d rarraba tare da sayar da maganin jabu laifukan da suka saba da Sashe na 1 (a) a cikin dokar jabun mahunguna ta NAFDAC wanda kuma idan laifin ya tabbata za a hukunta mutum karkashin Sashe na 3(1) (a).
Lauyoyin wadanda ake kara, Barista E. N. Ogbu da Usman Ashafa da S. M. Waziri sun nemi kotun ta bayar da belin wadanda ake kara.
Sai dai Alkalin Kotun, Mai Shari’a Simon Amobeda ya yi umarnin a tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali inda ya kuma dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Yuni 2024.
Jim kadan bayan fitowa daga kotun, Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa hukumarsu a shirye take ta sa kafar wando daya da duk masu aikata laifuffuka da suka shafi magunguna.
A cewarta “Bayan an kana mutanen an samu cewa ba a yi wa magungunan rajista da Hukumar NAFDAC ba, lambobin da ke jikin maganin na jabu ne”
Ta kuma bayyana cewa sun gano inda ake hada wadannan jabun magungunan wanda tuni suka rufe shi.
“Bincikenmu ya gano wurin da ake hada magungunan na jabu a garin Tafa a Jihar Neja wanda tuni muka rufe shi. An fallasa jabun magungunan bayan an samu bayanan da suka taimaka wajen kama mutanen”
Farfesa Adeyeye ta kuma jaddada kokarin da NAFDAC ke yi wajen raba al’umma da jabun magunguna inda ta kuma yi kira ga jama’a da zarar sun ga wani abu da suke zargi su gaggauta sanarwar hukumar don daukar matakin da ya dace
.