NAFDAC ta kone magununan Naira miliyan 15 a Kebbi

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) reshen Kebbi, ta kone gurbatattun magunguna da kayan abinci  na kimanin Naira miliyan 15.Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar NAFDAC reshen Jihar Kebbi, Garba Abubakar Adamu a lokacin kone magungunan da hukumar ta yi a cikin dajin Kola da ke karamar Hukumar […]

NAFDAC ta kone magununan Naira miliyan 15 a Kebbi
NAFDAC ta kone magununan Naira miliyan 15 a Kebbi

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) reshen Kebbi, ta kone gurbatattun magunguna da kayan abinci  na kimanin Naira miliyan 15.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar NAFDAC reshen Jihar Kebbi, Garba Abubakar Adamu a lokacin kone magungunan da hukumar ta yi a cikin dajin Kola da ke karamar Hukumar Birnin Kebbi.
Garba Abubakar Adamu ya ci gaba da cewa wadannan magungunna da  kayan abinci an kwace su ne a hannun ’yan kasuwa masu yawo a kan tituna da kuma wadanda ke da shaguna. Ya ce an kone magungunan ne saboda yawancinsu sun gama aiki wasu kuma ba su da rajista da hukumar ta NAFDAC.
Shugaban hukumar ya kara da cewa, duk kokarin da hukumar ke yi a kullum wajen yaki da masu wannan muguwar sana’a abin sai gaba-gaba yake yi, saboda haka ya nemi kananan hukumomin jihar su hada hannu  da Hukumar NAFDAC da   zimmar samar da kwakkwarar hanyar shawo kan wannan babban  lamari kasancewar kullum masu wannan  sana’a yawaita suke yi.
Ya ce hukumarsu tare da hadin gwiwar  jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya da masarautan jihar da  ’yan jarida sun  dukufa wajen tsince ire-ire wadannan magunguna da nau’in kayan abinci masu cutarwa.
A karshe ya nemi jama’a su rika kula a yayin da suka je sayen magunguna da nufin kauce wa sayen gurbatattun da  kuma wadanda wa’adin aikinsu ya kare don kauce wa kamuwa da cututtuka.