NAFDAC ta kwace maganin kara kuzarin jima’i

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ta kwace katon-katon na magungunan kara kuzarin jima’i a wata kasuwa a Legas. Jami’an Sashen Aiki da Cikawa na Hukumar NAFDAC ne suka kama maganin mai suna Japata, wanda ke cin ganiyarsa har a wurin masu yawon tallar magungunan gargajiya. Kudin Makamai: Kotu ta daure Doyin Okupe […]

NAFDAC ta kwace maganin kara kuzarin jima’i
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ta kwace katon-katon na magungunan kara kuzarin jima’i a wata kasuwa a Legas.
Jami’an Sashen Aiki da Cikawa na Hukumar NAFDAC ne suka kama maganin mai suna Japata, wanda ke cin ganiyarsa har a wurin masu yawon tallar magungunan gargajiya.

Hukumar ta ce gwajin da ta gudanar kan maganin da ta kama da kudinsa ya kai Naira miliyan takwas, ya nuna yana da hadari ga lafiyar dan Adam.

Rahotanni sun nuna jabun magunguna da da dama da ke cin kasuwarsu, musamman a karkashin gadoji a Legas ne hukumar a kama.

Sai dai yunkurin hukumar na kama babban dillalin maganin na Japata a Kasuwar Apongbon da aka kai samamen bai yi nasara ba, amma ta ce tana hakon sa.