Nafisa Abdullahi ta bukaci a rika taimaka wa marayu

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi wadda aka fi sani da Nafisa Sai Wata Rana ta bukaci jama’a su rika taimaka wa marasa galihu da marayu da kuma musakai.Jarumar wadda ta nanata muhimmanci taimako da sadaka da kyauta, ta bayyana haka ne a lokacin da take tattaunawa da Aminiya ta wayar tarho a ranar Litinin.A […]

Nafisa Abdullahi ta bukaci a rika taimaka wa marayu
Nafisa Abdullahi ta bukaci a rika taimaka wa marayu

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi wadda aka fi sani da Nafisa Sai Wata Rana ta bukaci jama’a su rika taimaka wa marasa galihu da marayu da kuma musakai.
Jarumar wadda ta nanata muhimmanci taimako da sadaka da kyauta, ta bayyana haka ne a lokacin da take tattaunawa da Aminiya ta wayar tarho a ranar Litinin.
A makon jiya ne jarumar ta ziyarci gidan marayu da ke Kaduna, inda ta rarraba kayayyakin masarufi da suka hada da shinkafa da taliyar Indomie da man gyada da sukari da Maggi da biskit da madara da sabulu da omo da man shafawa da sauransu.
Jarumar ta bayyana cewa ta shiga tashin hankali bayan ta ziyarci gidan marayun sakamakon yanayin da ta iske su a ciki. “Na shiga cikin tashin hankali bayan na ga halin da marayun suke ciki, suna bukatar taimako. Don haka akwai bukatar jama’a suka rika ziyartar gidajen marayu don su fahimci halin da suke ciki, sannan a rika taimaka musu domin da na kowa ne, ba a san wanda zai more shi ba,” inji ta.
Jarumar ta ja hankalin jama’a cewa duk wanda ya taimaki wani Allah Zai taimake shi, sannan wadansu za su taimake shi ko su taimaki ’ya’yansa.
Ta ce: “Sau da yawa mutane ba sa la’akari da cewa alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza, sai ka ga mutane kansu kawai suka sani, daga su sai ’ya’yansu, don haka idan mutum ya taimaki ’ya’yan wani, to wani ma zai taimaki ’ya’yansa, musamman tunda ba a san wane ne gawar fari ba. Kamar yadda ’ya’yan wadansu suka zama marayu, ’ya’yan mutum ma za su iya zama marayu, don haka mu ci gaba da taimaka wa marayu.”
Jarumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ziyartar gidajen marayu a fadin kasar nan tare da taimaka musu don ganin su jin dadi rayuwa kamar ’ya’yan da suke gaban iyayensu.
Nafisa ta kuma bukaci ’yan fim su rika ziyartar gidajen marayu da kuma taimakon marasa galihu, sannan ta bukaci a rika shirya fina-finai da ke nuna halin da marayu suke ciki da kuma fadakar da mutane muhimmancin taimakon marayu.