Nafisa ta soki gwamnatin Buhari kan kisan Zamfara

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, ta soki gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari game da daukan matakin gaggawa akan kisan gillan da ake yi wa jama’a  a wasu kauyuka na jihar Zamfara. Jarumar ta soki shugaban ne a kafar sada zumunta ta tiwita, inda ta bayyana matakin da shugaban ya dauka akan kisan mutum daya […]

Nafisa ta soki gwamnatin Buhari kan kisan Zamfara

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, ta soki gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari game da daukan matakin gaggawa akan kisan gillan da ake yi wa jama’a  a wasu kauyuka na jihar Zamfara.

Jarumar ta soki shugaban ne a kafar sada zumunta ta tiwita, inda ta bayyana matakin da shugaban ya dauka akan kisan mutum daya Kolade Johnson da ‘yan sandan Legas suka harbe, amma bai binciki kisan gillar da ‘yan bindigar Zamfara ke ci gaba da yi ba.