NAHCON ta mayar wa alhazai N5.3bn kan matsalolin Hajjin 2023
Hukumar aikin Hajji ta Ƙasa NAHCON ta buƙaci EFCC da ICPC su sanya ido kan yadda za ta gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 da ke tafe
Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta dawo da Naira biliyan 5.3 domin raba wa Alhazai saboda matsalolin da aka fuskanta a yayin aikin Hajjin 2023 da aka kammala.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa ta mayar da kuɗaɗen alhazan ne saboda rashin gamsuwa da wasu ayyukan da kamfanonin kasar Saudiyya suka gudanar musu, da ma ayyukan da ba su yi ba a lokacin aikin Hajjin.
Sanarwar ta buƙaci alhazan da suka sauke farali a 2023 su tuntuɓi hukumomin alhazan jihohinsu ko kamfanonin jiragen yawon da suka bi, domin karɓar kuɗaɗensu. Ta ƙara da cewa kowanne alhalin 2023 zai sami Naira dubu sittin da Naira tamanin.
Ta bayyana cewa ta miƙa Naira biliyan 4.47 ga hukumomin kula da jin daɗin alhazan jihohi domin raba ba alhazan da suka sauke farali a 2023.
- NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen da iyaye ke fuskanta wajen tarbiyyar ’ya’yansu
- An kama matashi kan luwaɗi da yara 12 a Jigawa
Kamfanonin jiragen yawo 192 da aka tantance kuma an ba su jimillar Naira miliyan 917 domin mayar wa alhazansu.
Ta ci gaba da cewa nan gaba kuma za a zo kan sauran kamfanonin da suka yi aikin Hajjin 2023 da ba su samu ba, bayan kammala aikin tantancewa.
Hukumar ta buƙaci maniyyatan 2025 da su fara biyan kuɗaɗensu domin tabbatar da kammala shirye-shirye da wuri.
Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya kuma bukaci hukumomin yaƙi da almundahana (EFCC da ICPC) su sanya ido a kan aikin, domin tabbatar da gudanar da shi cikin tsafta.