NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana
NAHCON ta ce tsawaita wa’adin wata dama ce ga maniyyatan da ba su kammala biyan kuɗin kujerar ba.
Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta sanar da tsawaita wa’adin karɓar kuɗin aikin Hajjin bana.
NAHCON ta ce daga yanzu zuwa 10 ga watan Fabrairu ƙofa a buɗe take ta ci gaba da karɓar kuɗin kujera ga maniyyatan da ke son sauke farali a bana.
Ana iya tuna cewa, da misalin ƙarfe goma sha biyun daren ranar Juma’a 31 ga watan Janairun 2025, ne wa’adin biyan kuɗin kujerun aikin hajjin bana ya cika.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar NAHCON ta ƙasa, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce tsawaita wa’adin wata dama ce ga maniyyatan da ba su kammala biyan kuɗin kujerar ba.
Hajiya Fatima ta kuma ce NAHCON ta buƙaci shugabannin hukumomin Alhazai na jihohi da su tabbatar sun bayar da haɗin kai na miƙa mata kuɗaɗen alhazan domin tanadar musu masauki a ƙasa mai tsarki.
Tun bayan cikar wa’adin na farko ne NAHCON, ta shaida wa BBC cewa, idan har akwai wani sabon bayani a game da ƙara wa’adin biyan kuɗin to hukumarsu za ta sanar.
NAHCON ta ce daga bayanan da suke samu daga jihohi kawo yanzu mutane sun biya kuɗinsu domin akwai ma waɗanda suka biya kuɗin da ya zarta wanda aka sanar sakamakon hasashen cewa kuɗin kujerar bana zai iya kai wa Naira miliyan 10.
“Yanzu irin waɗannan mutane da suka biya kuɗin da ya zarta na kujerar suna ta murna bayan sanar da kuɗin kujerar ta bana, kuma nan ba da jimawa ba za a mayar musu da sauran kuɗinsu bayan an cire wanda ya kamata,” in ji Hajiya Fatima.