NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kudin Hajjin bana
NAHCON tana da tazarar lokacin da bai wuce wata guda ba ta kammala biyan duk kudin maniyyan Hajjin bana.
Hukumar Kula da Harkokin Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta dauki matakin tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar Hajjin bana.
Cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar a wannan Talatar, ta ce an tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2024.
- Za mu kara soke lasisin wasu masu hakar ma’adanai a bana — Alake
- Jirgin sama dauke da mutane 378 ya kone a Japan
Ta ce an dauki wannan mataki ne la’akari damuwar da wasu malaman addini, hukumomin jin dadin alhazaina jihoho da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar domin tsawaita wa’adin.
Hajiya Fatima Usara ta ce maniyyatan da ke sha’awar sauke farali bana a kasa mai tsarki suna da damar sayen kujera a yayin da Gwamnatin Tarayya ta sahale a tsawaita wa’adin biyan kudin.
Ta kara da cewa, da wannan ne kuma Hukumar NAHCON ke tunatar da maniyyatan cewa Ma’aikatar Hajji da Umara ta Saudiyya ta tsayar da 25 ga watan Fabrairun 2024 a matsayin ranar da za ta rufe duk wasu shirye-shirye da suka danganci yi wa maniyyata rajista.
A cewarta, la’akari da wannan mataki, NAHCON tana da tazarar lokacin da bai wuce wata guda ba ta kammala biyan duk kudin maniyyan Hajjin bana.
Kazalika, ta ce NAHCON tana ci gaba da fadi-tashin ganin ta cimma muradun duk masu ruwa da tsaki duk da cewa tsawaita wa’adin da ta yi ya zarce lokacin da ta kayyade a jadawalin shirye-shiryenta kan aikin Hajjin na bana.
NAHCON ta ce shugabanta, Malam Jalal Ahmad Arabi ya mika godiyarsa ga malaman addini, hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki da suka ba da hadin kai har aka kawo wannan kadami.
Malam Arabi ya yi addu’ar samun nasara a duk shirye-shiryen da NAHCON ke yi har zuwa karshen Hajjin na bana.