NAHCON za ta sayar da sansanin alhazai

Hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) na shirin cefanar da sansanin alhazanta da ke Jihar Legas ga ‘yan kasuwa, shekara 20 bayan watsi da shi. Sansanin mai makwabtaka da filin jirgi na Murtala Muhammad shi ne matattarar maniyyata aikin Hajji a Kudu maso Yammacin Najeriya kafin kai su filin jirgin su wuce kasar Saudiyya domin sauke […]

NAHCON za ta sayar da sansanin alhazai

Hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) na shirin cefanar da sansanin alhazanta da ke Jihar Legas ga ‘yan kasuwa, shekara 20 bayan watsi da shi.

Sansanin mai makwabtaka da filin jirgi na Murtala Muhammad shi ne matattarar maniyyata aikin Hajji a Kudu maso Yammacin Najeriya kafin kai su filin jirgin su wuce kasar Saudiyya domin sauke farali; amma yawan cinkoson ababen hawa a jihar da ke kawo tsaiko wurin daukar alhazai ya sa aka yi watsi da sansanin na tsawon shekaru.

A ziyarar da ya kai sansanin, shugaban NAHCON Dhikrulahi Hassan, ya ce, “Za mu gayyato ‘yan kasuwa da za mu yi hadin gwiwa da su, mu ga yadda za su mayar da sansanin domin mu yi tarayya a cikin ribar da za a samu”.

Dhikrulahi ya ce hadin gwiwa da masu zuba jarin zai taimaka wajen daukaka darajar sansanin ta yadda zai amfani al’ummar Musulmin jihar Legas da ma Najeriya baki daya.

“Zai dauki lokaci amma duk wanda ya zo zai ga irin kayan da aka samar sannan ya sa kudadensa, kafin bayan lokaci kowannemu ya ci riba”, inji Dhikrulahi wanda ya jagoranci kwamitin amintattun hukumar.

“An yi watsi da aikin ba a amfani da shi tsawon shekaru. Shugabancina na da burin ganin an koma amfani da shi ta yadda cikin ‘yan watanni za a bude shi ga Musulmai da sauran al’ummar da ke Legas.