Na’ibin Babban Limamin Sabo Ibadan na biyu ya rasu
Da yammacin ranar Asabar da ta wuce ne Majalisar Sarkin Hausawan Ibadan ta bayar da sanarwar rasuwar Na’ibi na biyu na limamin babban masallacin Unguwar Sabo Ibadan Malam Saleh Bako da ake kira da Baba Ilori. Marigayi Malam Saleh Bako, ya rasu ne a gidansa da ke Unguwar Sabo bayan gajeruwar jinya. Ya rasu yana […]

Da yammacin ranar Asabar da ta wuce ne Majalisar Sarkin Hausawan Ibadan ta bayar da sanarwar rasuwar Na’ibi na biyu na limamin babban masallacin Unguwar Sabo Ibadan Malam Saleh Bako da ake kira da Baba Ilori. Marigayi Malam Saleh Bako, ya rasu ne a gidansa da ke Unguwar Sabo bayan gajeruwar jinya. Ya rasu yana da shekara 88 a duniya. Kuma ya bar mahaifiyarsa mai suna Hajiya Khadijat Bako mai shekara 115 da mata biyu da ’ya’ya 25 da jikoki 103.
Tun lokacin da aka bayar da sanarwar rasuwar marigayin, al’ummar Hausawa da ke zaune a wasu garuruwan jihohin Yammacin suka rika tururuwa domin halartar jana’izarsa a ranar Lahadi da safe.
Halifan Tijjaniya a Jihar Oyo Sheikh Ibrahim Inuwa ne ya jagoranci daruruwan Musulmi don yin Sallar Jana’izarsa a harabar Babban Masallacin Sabo. Daga bisani al’ummar Musulmi suka dunguma zuwa babbar makabartar Musulmin Arewa da ke Unguwar Sasa inda aka binne marigayin.
Sarkunan Hausawa na garuruwan da ke kusa da Ibadan da manyan malamai sun samu halartar jana’izar wacce ta samu halartar dimbin mutane da ake cewa ba a taba ganin yawan mutane kamar wannan ba. kannen marigayin da suka hada da Alhaji Nalado Bako da Alhaji Ahmadu Bako da Ustaz Ibrahim dan’azumi Bako, ne suka rika karbar bakuncin jama’a da suke zuwa domin ta’aziyyar marigayin a gidansa.