Na’ibin Limamin Jos ya bukaci a yafe wa juna

Mataimakin Babban Limamin Jos Sheikh Lawal Adam ya yi kira ga al’ummar Najeriya su rungumi akidar zaman lafiya da yafe wa juna. Sheikh Lawal Adam ya yi kiran ne a lokacin da ya jagoranci gabatar da Sallah a Masallacin Idi na Ali Kazaure da ke Jos a ranar Asabar da ta gabata.Ya ce wannan lokaci […]

Na’ibin Limamin Jos ya bukaci a yafe wa juna
Na’ibin Limamin Jos ya bukaci a yafe wa juna

Mataimakin Babban Limamin Jos Sheikh Lawal Adam ya yi kira ga al’ummar Najeriya su rungumi akidar zaman lafiya da yafe wa juna. Sheikh Lawal Adam ya yi kiran ne a lokacin da ya jagoranci gabatar da Sallah a Masallacin Idi na Ali Kazaure da ke Jos a ranar Asabar da ta gabata.
Ya ce wannan lokaci na Idin Layya lokaci ne na yi wa Allah godiya, don haka ana bukatar kowane Musulmi ya yafe wa dan uwansa ya nuna soyayya da jin kai da kauna gare shi.
Ya yi kira ga shugabanni su ji tsaron Allah kan jagorancin al’umma da aka ba su amana, su kuma iyaye su yi kokarin bai wa ’ya’yansu ilimin addini da na zamani.
Sheikh Adam ya yi kira ga matasa su guji shaye-shaye miyagun kwayoyi su zamanto masu biyayya ga iyayensu da dokokin kasa. Sai ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da ake fama da rikice-rikice.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi