Na’ibin Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna ya rasu

Alaramma Ibrahim Isa wanda ya dade a matsayin Na’ibin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna ya rasu ne a safiyar ranar Laraba a asibiti

Na’ibin Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna ya rasu

Allah Ya yi wa Na’ibin Limamin Babban Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, Malam Ibrahim Isah, rasuwa.

Alaramma Ibrahim Isa, wanda ya dade a matsayin Na’ibin Babban Limamin Masallacin Sultan Bello, ya rasu ne a safiyar ranar Laraba a Asibitin Garkuwa da ke Unguwar Sarki, Kaduna.

Kwamitin Gudanarwar na Masallacin Sultan Bello ya sanar da rasuwar tare da cewa, “Za a gudanar da Sallar Jana’izar Alaramma Ibrahim Isa bayan Sallar Azabar a harabar masallacin,” da ke Unguwar Sarkin Musulmi, Kaduna.

“Allah Ya jikan sa da rahama, ya kuma sanya shi a Aljanna Firdausi,” in ji sanarwar.

Marigayi Alaramma Ibrahim Isa ya shekara sama da 20 a matsayin Na’ibin Limamin Sultan Bello.

Yana daga cikin cikin masu jagorancin Sallar Juma’a da Sallar Tahajjud, kuma Allah Ya yi masa baiwar zakin murya wajen karatun Al-kur’ani.

Hakazalika, ya kasance yana jagorancin majalisin karatun Alkur’anin a masallacin bayan Sallar Asuba.