Naira biliyan 1.6 da aka alakanta ni da su kyauta ne ga coci – Tsohon yaron Jonathan
Wani tsohon Mai tallafa wa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan kan Harkokin Gidansa, Dokta Waripamo-Owei Dudafa, ya fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa ba ya da laifi kan zargin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) take yi masa na almundahana. Jami’in ya ce Naira biliyan daya da miliyan 600 […]

Wani tsohon Mai tallafa wa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan kan Harkokin Gidansa, Dokta Waripamo-Owei Dudafa, ya fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa ba ya da laifi kan zargin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) take yi masa na almundahana.
Jami’in ya ce Naira biliyan daya da miliyan 600 da Hukumar EFCC ta alakanta shi da su, ba na almundahana ba ne, illa kudi ne da aka tara wajen wata gidauniya ga cocin Angilkan na kauyen Otuoke a shekarar 2013, cocin da tsohon Shugaba Jonathan yake babban uba gare shi.
Tsohon mai tallafa wa tsohon Shugaban kasar ya ce, Cocin Angalika na kauyen Otuoke ya kafa gidauniya don gina Cibiyar Bunkasa Matasa ta St. Stephen a garin Otuoke, mahaifar tsohon Shugaban kasar.
Dudafa ya ce an kaddamar da gidauniyar ce Legas kuma mutane da dama sun bayar da kyautar kudi ciki har da Babban Mai kaddamarwa Yarima Arthur Eze, wanda ya yi alkawarin bayar da Dala miliyan 10, (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 800) da zai biya daki-daki.
Dudafa ya ce tsohon Shugaban kasar ya umarce shi ya rika bin alkawarin da Eze ya yi don karbowa.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya fara jawabin kariya a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas game da almundahanar Naira biliyan 1.6 da Hukumar EFCC ke zarginsa da ita. An gurfabar da Dudafa ne da akantansa a bankin Heritage Bank, Joseph Iwuejo.
Da yake bayar da shaidar kariyar, Dudafa, wanda lauyansa Mista Adegboyega Oyewole (SAN), ya jagoranta ya ce, “Bisa huldata da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, na san kudin na gidauniya ce da Cocin Angilika na kauyen Otuoke ya kaddamar don gina Cibiyar Matasa ta St. Stephens a Otuoke.”
Sai dai Hukumar EFCC ta fadi a washegari Talata cewa babu wata shaida da ta nuna Dudafa ya mika wani bangare na kudin da ake zarginsa ga wani coci.
A lokacin da lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya bukaci Dudafa ya gabatar da shaidar ya tura wani kaso na kudin ga cocin, sai ya ce, Jonathan ne kawai zai iya yin bayani a kan haka.
Kuma da aka tambaye shi ya fadi sunan Bishop din Cocin Angalika na Otuoke, sai Dudafa ya ce, “Ban sani ba, na yi hulda ce kawai da tsohon Shugaban kasar.”
Lauyan Hukumar EFCC ya gabatar da bayanan banki kan yadda aka karkatar da kudaden zuwa wasu kamfanonin Dudafa.