Naira biliyan 13 za a kashe wa feshin kwari —Nanono

Ministan Noma da Raya Karkara Muhammadu Nanono ya ce Gwamnatin Tarayyar ta amince a fitar da Naira biliyan 13 domin yaki da kwari a jihohi 12 da ke Arewacin Najeriya. Jihohi da za su amfana da kudin sun hadar da Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Yobe da jihar  Borno. Za […]

Naira biliyan 13 za a kashe wa feshin kwari —Nanono

Ministan Noma Sabo Nanono

Ministan Noma da Raya Karkara Muhammadu Nanono ya ce Gwamnatin Tarayyar ta amince a fitar da Naira biliyan 13 domin yaki da kwari a jihohi 12 da ke Arewacin Najeriya.

Jihohi da za su amfana da kudin sun hadar da Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Yobe da jihar  Borno.

Za a fitar da kudaden ne da nufin bunkasa harkokin noma tare da shirin kar-ta-kwana kan illar da annobar COVID-19 ka iya yi wa al’amuran noma a yankin Arewa.

A sanarwar da ya fitar a ranar Asabar 13 ga watan Yuni, Nanono ya ce Gwamnatin Shugaba Buhari ta ba da muhimmanci ga yakar matsalar farin dango da ka iya ketarowa daga kasashen waje.

Sanarwar ta kuma ce an kaddamar da aikin hana ketarowar tsuntsayen kasashen waje da ke lahanta amfanin gona a jihar Kebbi duba da mahimmancin jihar a bangaren noma.