Naira Biliyan 33: Kotu ta bada umarnin tsare Mompha a gidan yari
Alkalin babbar Kotun tarayya da ke Abuja Mohammed Liman, a safiyar yau Litinin ya bada umarnin a ci gaba da tsare Isma’ila Mustapha wanda aka fi sani da Mompha, bisa zargin almundahanar Naira biliyan 33 a gidan yari. Kotun ta bada wannan umarnin ne bayan ya ki amincewa da tuhumar da kotun ke yi masa […]
Alkalin babbar Kotun tarayya da ke Abuja Mohammed Liman, a safiyar yau Litinin ya bada umarnin a ci gaba da tsare Isma’ila Mustapha wanda aka fi sani da Mompha, bisa zargin almundahanar Naira biliyan 33 a gidan yari.
Kotun ta bada wannan umarnin ne bayan ya ki amincewa da tuhumar da kotun ke yi masa na laifuka 14 na almundahanar Naira biliyan 33.
Kotun ta sanar da ranar 29 ga Nuwamba don ci gaba da sauraran karar da yanke hukuncin belinsa.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annadi EFCC, ta gurfanar da Mompha bisa zarginsa da damfarar kudade ta kamfanin Ismalob Global Investment Ltd, daga shekarar 2015 zuwa 2018.