Naira dubu 56 a matasyin mafi karancin albashi ya yi daidai ko ya yi yawa?

kungiyar kwadago ta Najeriya ta nemi a kara wa ma’aikata albashi, inda mafi karancin albashi zai fara daga Naira dubu 56. La’akari da yanayin da kasar nan ke ciki, abin tambaya a nan shi ne, shin wannan adadi ya yi daidai ko kuwa ya yi yawa? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban inda suka bayyana ra’ayoyinsu […]

Naira dubu 56 a matasyin mafi karancin albashi ya yi daidai ko ya yi yawa?
Naira dubu 56 a matasyin mafi karancin albashi ya yi daidai ko ya yi yawa?

kungiyar kwadago ta Najeriya ta nemi a kara wa ma’aikata albashi, inda mafi karancin albashi zai fara daga Naira dubu 56. La’akari da yanayin da kasar nan ke ciki, abin tambaya a nan shi ne, shin wannan adadi ya yi daidai ko kuwa ya yi yawa? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban inda suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:

Ma’aikata sun cancanci fiye da haka
– B.M. Dzukogi

Abubakar Haruna, a Minna

Baba Muhammad Dzukogi: “Ina ganin ya dace ba ma Naira dubu 56 ba, kamata ya yi a biya fiye da dubu 56 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati. Saboda haka a ganina kungiyar kwadago ta yi jinkiri da tun tuni ya kamata ta nemi wannan karin.”

Ya dace kuma ina goyon baya – Isyaku Bala

Abubakar Haruna, a Minna

Isyaku Bala Ibrahim: “A ganina, abin da kungiyar kwadago ta nema na ba a biya ma’aikatan gwamnati mafi karancin albashi na Naira dubu 56 ya dace a wannan lokaci, musamman ma idan aka yi la’akari da tsadar rayuwa da kayan abinci da kuma kayan masarufi. Saboda haka ni ina goyon bayan haka.”

karin abu ne mai kyau – Shafi’u Idris

Rabilu Abubakar, a Gombe

Shafi’u Idris: “A gaskiya ni a matsayina na dan Najeriya, wannan aniya ta kungiyar kwadago abu ne mai kyau amma ni ina ganin kamata ya yi a ce Naira dubu sittin za a biya ba dubu 56 ba, domin dubu 56 ba za ta yi wa karamin ma’aikaci komai ba saboda ga biyan kudin haya, ga sayen ruwa, ga biyan kudin wutar lantarki. Idan kana da babur za ka sa masa fetur, nawa ka tsira da shi, kafin a yi maganar abincin da mutum zai saya a watan? Don haka a bai wa ma’aikaci Naira dubu sittin kawai, a nawa ra’ayin.”

Dubu 56 ya yi daidai – Sani Keeto

Rabilu Abubakar, a Gombe

Sani Keeto Gombe: “A gaskiya albashin Naira dubu 56 ya yi daidai saboda idan aka yi haka, karamin ma’aikaci shi ma lokaci ya yi ke nan da zai mori arzikin kasarsa kamar kowanne babban ma’aikaci. Ina amfani da wannan dama in yi kira ga gwamnati da ta saurari wannan kuduri na kungiyar Kwadago saboda alheri ne ba ga ma’aikacin shi kadai ba, har da duk wani dan kasuwa da jama’ar kasa. Uwa uba ma, mu ne malaman makaranta da muka fi kowanne ma’aikaci shan wahala, amma ’yan siyasa suke kwashe kudin ga baki daya.”

Dubu 56 sun yi yawa – Abdulmalik Aminu

Musa Kutama, a Kalaba

Alhaji Abdulmalik Aminu Kafinta: “Gaskiya halin da tattalin arzikin kasa ya shiga kudin ya yi yawa amma yana da kyau idan har za a amince a biya din. Amma ina laifi a ce an bar shi Naira dubu 30 ko 35 saboda tattalin arzikin Nijeriya ya yi kasa sosai amma karin dubu 56 mafi karancin albashi za a shiga matsala saboda Gwamnatin Tarayya ba ta da kudi.”

karin ya dace – Malami Ibrahim Sakkwato

Musa Kutama, a Kalaba

Alhaji Malami Ibrahim kofar Atiku: “Ga irin halin da ake ciki, kowane magidanci yake ji a jikinsa da ma sauran ’yan Najeriya; karin babu laifi, ya yi. karin a gaskiya ga kowane karamin ma’aikaci ya yi daidai saboda buhun gero da sauran kayan abinci farashinsu ya karu, maganar dubu 56 din nan da ake son a yi kari babu laifi, ya yi.”