Najeria guda ce…

A yanzu dai gwamnatin tarayya ta fara nuna damuwarta game da kasassabar da wasu gwamnonin jihohin Kudu ke yi na neman tilasta wa‘Yan Arewa da ke yankunansu, walau tsoffin zama ko masu zuwa cirani, su yi rajista don a tantance ‘yan kungiyar Boko Haram daga cikinsu, har ma ta nemi Majalisar tsoffin shugabannin kasa da […]

Najeria guda ce…
Najeria guda ce…

A yanzu dai gwamnatin tarayya ta fara nuna damuwarta game da kasassabar da wasu gwamnonin jihohin Kudu ke yi na neman tilasta wa‘Yan Arewa da ke yankunansu, walau tsoffin zama ko masu zuwa cirani, su yi rajista don a tantance ‘yan kungiyar Boko Haram daga cikinsu, har ma ta nemi Majalisar tsoffin shugabannin kasa da gwamnoni masu ci da tsoffin manyan alkalai da su hallara a Abuja a mako mai zuwa don tattauna wannan abin takaicin.
Wannan al’amari ya tayar da kura, a can wajajen da aka tsiri haka da kuma inda wadancan mutanen da aka yi dominsu suka firfito. Babu shakka wannan wata sabuwar shegantaka ce, ko kuma a ce fitinar da ake son tayarwa da gangan don yamutsa kasar, har ta kai zaman lumana tsakanin al’ummominta ya faskara. Wannan abu ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan, kuma jama’ar kasar gaba daya ba su amince da haka ba, illa kawai wadanda suka tsiri wannan abu don tsananin rashin hankali da hangen nesa da kuma watsi da abubuwan da za su je, su kuma komo.
A dangantakar da ke wanzuwa tsakanin al’ummomi irin daban-daban na kowace kasa, kwaryar da ta je, ita ce kuma takan dawo, ma’ana cuta ko alherin  da wasu jama’a suka kulla yakan komo gare su, kaman yadda kaikayi ke komawa kan mashekiya. Babu wata al’ummar da ake  tarayya  da ita a harkokin  zamantakewa da za ta bugi kirji ta nemi muzgunawa wasu kabilu sa’annan ta yi tsammani ta yi ke nan, babu wani abin da zai biyo baya, domin  ita shafaffiya da mai ce, `ta fi karfin kowa.
Jihohin Enugu da ta Imo a shiyyar Kudu-maso-Gabas da kuma Jihar Lagos a shiyyar Kudu-maso Yamma sun dukufa kan kuntata wa mutanen Arewa, musamman ma Hausa-Fulanin ta neman ganin bayansu, da mayar da rayuwarsu mawuyaciya. Tuni har Jihar Enugu ta tsara wani katin izni ga Hausa-Fulani don ‘yan Arewa mazauna can, ko masu  gudanar da harkokin kasuwanci da sauran ma’amaloli. Hakan kuwa ya biyo bayan tozarci da wulakancin da aka yi wa wasu Hausawa sama da 480  ne a Jihar Abia, sa’ilin da suke kokarin shiga jihar don cin arziki, sai aka kakkame su, aka yi ta tijara da su, daga karshe aka hana su zama a jihar, aka mayar da su garuruwansu, kamar wasu bakin haure.
Abin takaici game da haka shi ne lokacin da ake wannan al’amari babu wani gwamnan Arewa da ya nemi mayar da martani ga ‘yan Jihar Abia da ke kwararowa tasa jihar a kullum don gudanar da harkokin arziki. Ai idan da wani ya yi haka da al’amarin bai tabarbare ba, da kuma wasu gwamnonin Kudu  ba su dau hannu ba. To har yanzu dai babu wani gwamna daga Arewa  da ya bugi kirji, ya yi haka, kaman yadda  wasu takwarorinsa a Kudu suka yi, kuma sama da kasa ba su hade ba sakamakon haka. Ana ji ana gani aka kyale su, sai daga baya ne gwamnati take zazzare idanu, tana gargadI don kar hakan ya faru a yankin Arewa.
 Dangane da haka ne wasu kungiyoyin matasa a Arewa suka dumfari fadar Maimartaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, suka fayyace masa manufarsa ta baiwa ‘yan Kudanci, mazauna Jihar Kano,  wa’adin mako biyu su tattara ya-na-su-ya-nasu, su san inda dare zai yi masu, kuma  wata kungiyar ta nufi majalisar dokokin Jihar Kano da shawarwar da take so a mayar da ita dokar da za ta bayar da ikon yi wa ‘yan Kudancin da ke jihar, da masu son zuwa nan gaba, takardun iznin zama don a magance masu aikata ta’asa irin ta fashi da makamai da satar bil-adama da kakkafa masana’atar  haihuwar jarijarai don sayarwa, da dai sauransu.
Wadanan batutuwa ba su yi wa ‘yan kudu dadi ba, domin an ce wanzami bai son jarfa. Sai ga shi nan Sarakunan al’ummomin kudanci sun ziyarci mai martaba Sarkin Kano, suna nuna masa rashin amincewarsu da wadannan manufofin da matasan jihar ke so a dauka, suka kuma nemi a tsawata masu, alhali kuwa lokacin da ake takurawa Hausa-Fulani a  yankunansu ba su yi wa gwamnonin jihohin Kudu kashedi ba.
Wadannan abubuwan da dukkan bangarorin biyu suka yi sun sabawa kundin tsarin mulkin da ya ba kowane kasa ‘yancin walwala da walawa a ko ina ya kasance a kwaryar tarayyar Najeriya, ba tare da wata tsangwama ko kyara ba. Ya kamata mutanen kudu su tuna fa da yawansu sun yi kaka-gida a  Arewaci, kuma harkokin kasuwanci da guraben aiki a manyan kamfanoni duk ‘yan kudu ne suka kankane, kuma ‘yan Arewa babu abin da suka iya game da haka, duk kuwa da ganin cewa ‘ya’yansu bila-adadin da suka kware a harkar kasuwancin, suka kuma yi digiri da digirgir a kowane fannin ilmi   suna zaman kashe wando a gidajen iyayensu, ba su da aikin yi, kamar yadda ‘yan Arewa da ke Kudu ba su samun aikin kirki komai kwarewarsu da ilminsu, sai dai aikin karfi da na leburanci. Ya kamata dai a tunatar da cewa Najeriya fa kasa guda ce, amma kowa ya san gidan ubansa..