NAJERIYA A YAU: Yadda Aminu Kano ya fara daukar mace mataimakiyar dan takarar shugaban kasa
Dalilan da Malam Aminu Kano ya zama na farko wajen zaben mace ta yi masa mataimakiyar shugaban kasa
Domin sauke shirin latsa nan
Bayan shekara 38 da barin duniya, ’yan Najeriya na ci gaba da tunawa da Malam Aminu Kano a bangarori da dama.
Jama’a da dama na kallon Malam Aminu Kano a matsayin wanda ya sauya akalar siyasar Najeriya ta hanyar zama mutum na farko da ya zabi zabi mace a matsayin ’yar takararsa ta mataimakin shugaban kasa.
Shin kawo yanzu, burin Malam din na ganin an dama da kowa da kowa a fagen siyasa ya cika kuwa?