Najeriya a 58: Ko kwalliya ta biya kudin sabulu?
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 58 da samun ’yancin kai. Wannan karon Gwamnatin Tarayya ta inganta bikin ranar matuka. Duk da cewa rana ce ta murna, wadansu suna ganin cewa babu wani abin murna a ciki domin har yanzu kasar na nan jiya-i-yau. Wannan ne ya sa wakilanmu suka zagaya domin jin […]
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 58 da samun ’yancin kai. Wannan karon Gwamnatin Tarayya ta inganta bikin ranar matuka. Duk da cewa rana ce ta murna, wadansu suna ganin cewa babu wani abin murna a ciki domin har yanzu kasar na nan jiya-i-yau. Wannan ne ya sa wakilanmu suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan wannan rana ta murnar samun ’yancin kai:
Ba a samu wanici gaba ba – AbdurRahman Auwal
Daga Bashir Liman, Jos
AbdurRahman Auwal, dan siyasa, dan kwangila kuma marubuci, ya bayyana cewa har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba duk da cewa Najeriya ta shekara 58 da samun ’yancin kai.
“Idan ka lura za ka ga babu abin da ya sauya, hanyoyi sun lalace, babu asibitoci, makarantu sun lalace, babu ruwan sha, babu wutar lantarki, ana fama da talauci da fatara. Kama- karyar da ake yi lokacin soja har yanzu ana ci gaba da yi a wannan mulkin na dimokuradiyya da ake yi, a yanzu ba a bin doka da oda kamar lokacin mulkin mallaka ko mulkin soja.
Talakawa suna cikin wani hali. Kowa na yin abin da ya gama, babu wani ci gaba da aka samu. Kada ka manta har yanzu mutane irin su Jeremiah Useni ne suke so su mulki mutane, ka ga babu wani ci gaba da aka samu ke nan.”
Babu abin murna Najeriya a 58 – Haruna Yusuf Abba
Daga Bashir Liman, Jos
Haruna Yusuf Abba, dan siyasa kuma mai rajin kare ’yancin dan Adam ya bayyana cewa babu abin murna don Najeriya ta cika shekara 58, “Domin rashin aikin yi da talauci da yunwa da matattun hanyoyi da yajin aiki a makarantu da rashin dauwamamiyar wutar lantarki da tabarbarewar ilimi da harkar lafiya da rashin tsaro da kashe-kashe sun sanya kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Idan aka lura a yanzu abubuwa na ci gaba da tabarbarewa tun kafin dawowar dimokuridiyya wato tun daga 1999 har yau abubuwa sai kara tabarbarewa suke yi. Mulkin dimokuradiyya bai amfani talaka da komai ba sai wahala da kara bautar da su. Tun da aka samu ’yancin kai a shekarar 1960 har yanzu ba mu samu makama ba, sai kara lalata gudunmawar da shugabannin da suka shude muke yi, a yanzu miyagun shugabannin sun yi yawa. Allah Ya ba mu shugabanni masu kishi da kaunar kasa, masu yunkurin yi wa kasa hidima.”
Kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba – Umar Farouk Ahmed
Daga Ahmed Ali, Kafanchan
Umar Farouk: “A ganina har yanzu da sauranmu idan muka yi la’akari da kasashen da muka samu ’yancin kai tare ko kuma kusa da juna. Ta wasu fannonin an samu ci gaba amma a hakika mu har yanzu kwalliya ba ta biya mana kudin sabulu ba sai dai mu ce sabulu ne ya biya kudin kwalliya domin mutanen da kasar nan ta yi musu sutura suka zama wadansu su ne kuma suke tadiye kafar wadansu. A Najeriya ne har yanzu ’yan siyasa ba yin kamfen da salon ’yan Jamhuriyya ta Farko; za ka ji suna cewa idan aka zabe su za su samar mana da ruwan sha da tituna da wutar lantarki da gyara makarantun firamare da kananan asibitoci wanda kamata a ce yanzu mun yi nisa. Gaskiya da sauranmu tukuna.”
Har yanzu akwai gyara – Muhammad Adamu Musa
Daga Isiyaku Muhammed
Muhammad Adamu Musa: “Matsalata ita ce rashin tsari a Najeriya. shekara 58 sun isa kasa ta zama cikakkar kasa ba kamar yadda Najeriya take ba a yanzu. gaskiya wadansu daga cikinu ba sa jin dadin yadda abubuwa suke tafiya a kasar nan. Don haka ban ga wani abin murna ba sosai. Ci gaban kasar nan gaskiya yana tafiyar hawainiya.”
An samu ci gaba sosai – Sani Abdullahi
Daga Isiyaku Muhammed
Sani Abdullahi: “Gaskiya a tawa fahimtar an samu ci gaba sosai. Muna jin labarin yadda iyayenmu da kakanni suka sha wahala a zamanin rayuwarsu, amma mu yanzu muna samun sauki sosai. An samu ci gaba sosai a harkar mulki, an samu ci gaba a harkar noma da kiwon lafiya da sauransu. Don haka wannan rana ta isa mu yi murna.”
Kwalliya ta biya kudin sabulu – Alhaji Mudi Shafi’u
Daga Ahmad Ali, Kafanchan
Alhaji Mudi Shafi’u Tahir: “A gaskiya zan iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu saboda ficewarmu daga bauta ma ba karamin ci gaba ba ne, na daya ke nan. Saboda mutumin da ya san me ake kira bauta, zai san muhimmamcin ’yanci a rayuwa domin kalmar ’yanci kadai abin alfahari ne a duniyar nan. A sanadiyyar ’yanci yanzu muna da kwararru kuma gogaggun ’yan kasa da za a iya fafatawa da su a kusan kowane fanni na ilimi a duka duniyar. A takaice komai lalacewa dai ’yanci ya fi bauta ko da a ce ba komai ne ke tafiya dari bisa dari ba. Idan kuma ana batun ko me muka tsinana wa kanmu ne bayan samun ’yanci, sai in ce ai shgabanninmu na farko kafin a samu gurbatattu sun yi aiki sosai wajen gina kasar nan.”