Najeriya: A ina matsalar take?

Daga Tukur Musa Fagge Babban abu mafi ban tsoro game da halin da muka samu kanmu a ciki a Najeriya shi ne, hali na fatar da talauci da tabarbarewar harkokin tsaro ta inda ’yan ta’adda za su iya sace yara a jihohin da suke cikin dokar ta-baci! Ilimi ya tabarbare tun daga Firamare har zuwa […]

Najeriya: A ina matsalar take?
Najeriya: A ina matsalar take?

Daga Tukur Musa Fagge

Babban abu mafi ban tsoro game da halin da muka samu kanmu a ciki a Najeriya shi ne, hali na fatar da talauci da tabarbarewar harkokin tsaro ta inda ’yan ta’adda za su iya sace yara a jihohin da suke cikin dokar ta-baci! Ilimi ya tabarbare tun daga Firamare har zuwa Jami’a, da rashin ingantaccen tsarin kula da lafiyar jama’a! da sauran tarin matsalolin da suka dabaibaye mu ta ko’ina. Abin da ya fi ba ni tsoro, shi ne, yaushe za a samu gyara ko sauyi? Idan muka dubi yadda tarbiyyar mafi yawan ’yan Najeriya ta zama gafiya tsira da na bakinki, kowa fafutika yake yi ya samu wata dama don ya hau tudun mun tsira daga farmakin kirkirarren bakin talaucin da ya mamaye mu! Kusan wannan shi ne tu8nanuin mafi yawan ‘’yan Najeriya.Halin da ake ciki na matsi da waiwai, ya zama abin tattaunawa ko da yaushe a tsakanin al’ummar wannan kasa, amma adalcin da ya kamata mu yi wa kanmu shi ne mu duba a ina matsalar take? Kuma ta yaya za mu gyara? Kodayake mafi yawa an fi dora alhakin matsalolin kacokan a kan shugabanni, kasancewar su ne Allah ta’ala ya dora wa alhakin jagorancin al’umma.
Gaskiya ne, shugabanni su ne ke dauke da kaso mafi yawa da fadawar al’ummar cikin halin da ake ciki, amma sauran jama’a kuwa kowa yana da tasa gudunmuwar, ba wai ina nufin in fito da laifuka, ko in ce gudunmuwar da kowa ya bayar gurin jefa al’umma cikin mawuyacin hali ba, domin wannan wani abu ne da an sha tattaunawa a kansa, kuma ana ci gaba da tattaunawa a kansa.
Abin damuwar shi ne yadda kowa baya duba laifinsa, ko gudunmuwar da yake bayarwa wajen kara danna al’umma cikin matsala. Matukar ba za mu yi nazarin matsalolinmu ba, kuma ba za mu duba laifinmu mu gyara ba, to, mu daina fita daga cikin halin da muka tsinci kanmu.
Ya kamata mu fada wa kanmu gaskiya cewa tun daga kan shugabanni da sarakuna da malamai da ’yan siyasa da ’yan boko da ’yan kasuwa da talakawa kowa yana da kaso cikin jefa al’umma a mawuyacin hali. Kuma mu sani Allah ta’ala ba zai canza mana ba, har sai mun canza da kanmu! Sannan kuma mu sani duk wata kasa da ta ci gaba a kowane fanni a duniya, sia da kowa ya sanya hannu – ya bayar da kyakkyawar gudunmuwa!
Sai kowa ya yi aiki tukuru, ya tsare gaskiya da amana a kan aikinsa ko sana’arsa da mu’amalarsa, matukar akwai dandanzon zalunci da karya da hassada da kyashi da munafunci da annamimanci da jahilci da sauran miyagun dabi’u cikinmu, to, lallai za mu yi ta zama cikin halin ha’ula’i.
Babban abin da yake gyara daidaikun mutane ko kuma al’umma ta zamo al’umma tagari shi ne imani; wato mutum ya san dalilin zuwansu duniya, kuma ya san cewa akwai wata rana da Mahalicci ya tanada don yi wa bayi sakamako bisa gwargwadon abin da suka aikata.
Samun ingantaccen imani a kowane addini mutu8m yake zai sanya masa tsoron Allah ta’ala tare da karfafarsa a gurin yin ayyukan da za su kyautata rayuwar al’umma don ya samu kyakkyawan sakamako.
Haka kuma wancan imanin zai hana shi yin duk wani abu da zai cutar da al’umma, don gudun samun mummunan sakamako a waccan rana.
Al’umma na iya gyaruwa matukar mun tsaya tsakani da Allah, mun yi aiki tukuru mun bi dokokin Allah ta’ala. Idan har da gaske muke yi muna neman mafita dga cikin matsalolin da suka kewaye mu, to, sai kowa ya yi wa kansa duba na tsanaki, ya ga me yake yi wanda yake bayar da mummunar gudunmuwar wajen jawo wa al’umma zaman dabaro cikin wannan shu’umar matsala wacce taki ci, ta ki cinyewa, ya kuma kuduri aniyar gyara tsakaninsa da Allah buwayayyen sarki.
Daga karshe lallai ya kowa ya sani cewa matsalar Najeriya ba mutum daya ba ne ya assasata ba, a’a dukkanmu muna da gudunmuwar da muka bayar wajen jefa wannan al’umma cikin halin kaka-ni-ka yi, saboda haka dole kowa ya koma ga mahaliccinsa, ya tuba daga aikata zunubai. Da fatan Allah Ya kawo mana dawwamammen zaman lafiya a kasar mu; Allah Ya amintar da mu jihohin mu da kasarmu. Allahumma amin.
Tukur Musa Fagge, ya rubuto makalarsa daga birnin Kano, a iya tuntubarsa ta +234805836601.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya