Najeriya a shekara 57: Ko ya kamata mu ci gaba da zama a dunkule ko kowa ya kama gabansa?
A daidai lokacin da Najeriya ta cika shekara 57 tun samun ‘yancin kai daga mulkin mallaka. Inda mutane k eta tofa albarkacin bakinsu kan nasarori ko akasanin haka da aka samu tun samun ‘yancin kan. Sai dai kuma, kasar na fuskantar kalubale daga masu yunkurin ballewa musamman ‘yan kabilar Ibo. Hakan yasa wasu daga yankin […]
A daidai lokacin da Najeriya ta cika shekara 57 tun samun ‘yancin kai daga mulkin mallaka. Inda mutane k eta tofa albarkacin bakinsu kan nasarori ko akasanin haka da aka samu tun samun ‘yancin kan. Sai dai kuma, kasar na fuskantar kalubale daga masu yunkurin ballewa musamman ‘yan kabilar Ibo. Hakan yasa wasu daga yankin Arewa suke ganin cewa kawai a barsu su kama gabansu tunda bas a so su zauna a matsayin ‘yan Najeriya. Wannan ne yasa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin tab akin mutane, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:
A ci gaba da zama a dunkule – Salamatu Sani
Ahmed Garba Mohammed a Kaduna
Salamatu Sani: A gaskiya na goyi bayan Najeriya ta ci gaba da zama a matsayin kasa dunkulalliya ba tare da wani sashe ya balle ba. Dalilin fadin haka kuwa shi ne duk abin da aka ce a yi shi a dunkule ya fi a ce za a yi shi ne a ware. Kamar yadda karin maganar Hausawa ke cewa ne “tsintsiya madaurinki daya”. Tsintsiya daya ba za ta yi shara ba, amma idan ta dunkule za ta share duk wani abin da ba a bukata, to tamkar irin wannan karin magana ne ga kasata Najeriya idan muka ci gaba da zama a dunkule, to duk matsalolinmu za mu magance su ba tare da wata matsala ba, idan kuwa muka ce kowa zai kama gabansa ne, to tilas ne a samu baraka ta yadda wasu za su samu damar shigowa don rarraba kawunanmu. A takaice dai zama a dunkule ya fi zama a ware.
Ya kamata mu ci gaba da zama kasa daya – Khadija Lawal
Daga Bashir Liman, a Jos
Khadija Lawal Kwargana: Ya kamata mu ci gaba da zama a matsayin kasa daya, domin ba mu yi yawan da za a ce an raba kasar ba, idan yawa ne ba mu kai kasar China da Indiya ba; idan ma batun yawan addini da kabila ake ba mu kai su wadannan kasashen da na lissafo ba, amma da yake suna da kishin kasa, sun kuma hada kansu ba sa batun raba kasa.
Kowa burinsa ya ga yadda zai taimaka kasarsa ta ci gaba. Don haka a Najeriya ba batun raba kasa za a yi ba, batun shugabanci nagari da kuma kishin kasa za a yi, idan muka hada kanmu za mu fi samun ci gaba, maimakon rabuwarmu.
Bai kamata kowa ya kama gabansa ba – Muhammed Adamu Musa
Isiyaku Muhammed
Muhammed Adamu Musa: Bai kamata kowa ya kama gabansa ba saboda matsalar Najeriya a kan yawa bane, yawancin matsalar ya ta’allaka ne da halayen ’yan kaasar. Koda za a raba Najeriya 774, matsalolin da muke fuskanta ba za su bar mu ba har sai mun gyara halayenmu. Mun dan samu ci gaba, amma idan mutum ya lura da kyau, zai ga cewa ya kamata ace mun wuce inda muke a yanzu.
Zaman tare ya fi – Sadiya Auwal Garko
Ahmed Garba Mohammed a Kaduna
Sadiya Auwal Garko: A ganina idan aka zauna tare ci gaba ya fi samuwa saboda idan ana tare ne ake fito da sababbin dabaru na cigaban tattalin arzikin kasa sannan idan aka tafi tare za a fi samun ci gaba mai ma’ana kamar yadda da wuya kasashen waje masu neman wargaza kan kasar nan su samu nasarar yin haka. Don haka zaman mu tare ya fi a ce kowa ya kama gabansa. Yau shekara 57 da samun ’yancin kai, da ba mu samu nasarar da muka samu ba, idan da a ware muke.
Rabuwarmu ba za ta haifar mana da da mai ido ba – Suleiman Dabo
Daga Bashir Liman, a Jos
Suleiman Dabo Boro: Ban taba ganin kasar da yawanta yake neman haddasa fitina kamar Najeriya ba, to ina so mutane su sani rabuwarmu ba za ta haifar mana da da mai ido ba. Yanzu ka duba kabilar Igbo suna takalma da sana’ar karafa da samar da manja da sauransu, mu a nan muna noma da kiwo, idan muka hada kanmu za mu samu nasarar da ba a zato, kuma tattalin arzikinmu zai inganta.
Mu fahimta bambanci addini da kabila ba shi ne matsalar ba,; matsalar rashin kishin kasa ne, sannan ’yan siyasa suna gwara kanmu don wata manufarsu, ni dai a nawa ra’ayin na fi so mu zauna kasa daya.
Bai kamata a raba ba – Mujahid Abdullahi danbayi
Isiyaku Muhammed
Mujahid Abdullahi danbayi: A nawa ra’ayin, gaskssiya ina ganin a gyara inda aka tabbatar yana haifar da matsalar da ta haifar da barazanar rabewar ya fi muhimmanci maimakon a raba.