Najeriya a shekaru 54 da ’yancin kai: An samu ci gaba ko akasi?
A makon jiya ne aka gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 54 da samun ’yancin kai. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon zamanin nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa akasin haka? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane kuma ga abin da suke cewa: Babu wani ci gaba – Sani Musa A.A. […]
A makon jiya ne aka gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 54 da samun ’yancin kai. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon zamanin nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa akasin haka? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane kuma ga abin da suke cewa:
Babu wani ci gaba – Sani Musa
A.A. Masagala, a Benin
Alhaji Sani Musa Ringim: “A ganina kuma abin da na fahimta game da batun ci gaba ko rashin ci gaba a cikin shekaru 54 da Najeriya ta samu ’yanci daga Turawan mulkin mallaka na Ingilan, idan ana maganar ci gaba na gaskiya, to lallai babu wani ci gaba da za mu daga hannu mu ce mun samu ban da kasha-kashen rayuka da muke fama da shi, wanda gwamnati ta kasa shawo kansa. Don haka ina ganin babu wani mutum mai hakali da basira da zai fito a gaban al’ummar Najeriya a cikin halin da kasar take ciki na rashin tsaro ga kuma cin hanci da rashawa da talauci da rashin aikin yi tare kuma da yawan yara kimanin miliyan goma ko fiye suna fama da jahlici da rashin kulawa daga gwamnati, sannan a ce an samu ci gaba. Don haka batun ci gaba sai dai nan gaba.”
Akwai ci gaba kadan – Ibrahim Muhammad
A.A. Masagala, a Benin
Malam Ibrahim Muhammad Sumaila: “Ni a hakikanin gaskiya, yadda nake ganin lamarin shi ne; a wani bangare za an samu wani abu irin mai kama da ci gaba. Misali, Najeriya ta samu karuwar al’umma, sannan masu ilimi sun karu duk da cewa wasu ba su aiki da wannan ilimin, domin kawo ci gaba a cikin kasarmu. Sai kuma ci gaba na yawan tashe-tashen hankula, duk da cewa kasar tana da dimbin arziki amma zalunci ya janyo talauci sai kara habaka yake yi. Sai kuma batun ci gaba na kasuwanci mai kama da ci gaban mai hakar rijiya, domin wannan ci gaban ya tsaya ne tsakanin manyan ’yan kasuwa, bai kai ga kanana ba. Kuma bangaren shugabancin kasa ma an samu ci gaba na cin hanci da rashawa, wannan ya sa zalunci ya samu gindin zama da ci gaba daga nan kuma sai tattalin arziki ya ci gaba da kara shiga cikin wani yanayi da talaka ba ya gani akasa. Ga baki daya za mu iya cewa wannan mai sauki ne idan muka yi la’akari muka duba fannin da ya shafi tsaro da yake ci gaba da tabarbarewa.
An samu ci gaba sosai – Nuraddin Kabiru
Nasiru Bello, a Sakkwato
Nuraddin Kabiru: “An samu ci gaba sosai in ka yi la’akari da inda aka fito. A can baya jami’a nawa muke da su a duk kasar nan kuma yanzu fa? Dawo ka dubi hanyar mota da ita kanta motar, inda muka fito manyan hanyoyi a jihar nan ba su wuce biyar ba amma yanzu sun fi ashirin kuma cikin tsari mai kyau ba wata hatsaniya. Sha’anin lafiya ma haka, asibitoci sun yawaita tare da likitocinsu. Kai na gajarta maka labara, ba wani bangare da ba a samu ci gaba ba a wannan shekaru da muka yi na ’yanci sai dai ruwa ba gudu, ci gaban bai kai na fada tare da bugawa a jarida ba, namu ne na cikin gida kawai.”
Babu wani alfanu ko ci gaba da aka samu -Kwamared Murtala
Nasiru Bello, a Sakkwato
Kwamared Murtala S. T: “Babu wani alfanu ko ci gaban da aka samu a wannan shekaru na samun ’yancin kai daga Turawa. Da ma ba a samu ba a zatona da mun samu ci gaban da muke bukata. Wato talakan kasar nan ya fi karfin abincinsa da tufafi da wurin kwana. Abin takaici da ban haushi a kasar nan, shugabaninmu ba su kyale mu da wahalar da muke ciki ba kawai sai tashin hankali ya addabe mu, kullum cikin fargaba muke musamman ’yan uwanmu a Maiduguri da Adamawa da Yobe. Da wannan matsala da kasar nan take ciki har wani ya zo mana da zancen an ci gaba, ai wannan wasan yara ke nan, wanda mu ba za mu bi wannan ayarin ba, kada magenmu ta sha mana kasari.
Najeriya ba ta ci gaba ba – Umar danladi
Rabilu Abubakar, a Gombe
Umar Abubakar danladi: “To idan muka duba kasashen da aka ba mu ’yancin kai tare da su rana daya, wadanda sun ci gaba ta fannoni daban-daban, musammam ma a bangaren kimiyya da fasaha amma mu Najeriya an bar mu a baya. Idan aka duba kasar Indiya, tana iya kera jirgin sama da sauransu, mu kuma Najeriya fa wane ci gaba muka samu? Idan aka duba abubuwan da Turawan mulkin mallakar suka bar mana irin hasken wutar lantarki da ilimin zamani mai inganci, duk mun yi watsi da su, to ina ci gaban yake?
An samu ci gaba a Najeriya – Muktari Bappah
Rabilu Abubakar, a Gombe
Muktari Ibrahim Bappah: “Ni a ganina, Najeriya ta samu ci gaba a wadannan shekaru 54 da samun ’yancin kai amma ba shugabaninmu na yanzu ba ne suka kawo ci gaban ba, zamani wanda dole ko ana so ko ba a so sai an tafi da zamanin. Idan aka lura, akwai arziki sosai a kasar, akwai kuma ci gaba ta hanyar kimiyya wadanda duk zamani ne ya zo da su kuma dubi duk da halin kunci da ake ciki, wasu kuma yanzu suke samun arzikin. Ka ga ba yadda za a yi a yi jam’i, a ce ba arziki ko ci gaba ba a Najeriya.
Abin bakin ciki shi ne, duk da arzikin da ake da shi da ci gaban da zamani ya kawo, mana akasarin ’yan Najeriya na fama da rashin ci gaba da talauci duk da cewar ita kasar ta ci gaba.”