Najeriya a Shekaru 54 Gwanda Jiya Da Yau!

Wani rubutuna da na yi a watan da Oktoban shekarar dubu biyu da sha uku (2013) da ta gabata, wanda daya daga cikin abokaina na facebook ya sake posting dinsa a 1/10/2014, shi ya ja hankalina matuka ga yin wannan rubutu na yau, da Najeriya ke murnar cika shekaru 54 da samun yancin cin gashin […]

Najeriya a Shekaru 54 Gwanda Jiya Da Yau!
Najeriya a Shekaru 54 Gwanda Jiya Da Yau!

Wani rubutuna da na yi a watan da Oktoban shekarar dubu biyu da sha uku (2013) da ta gabata, wanda daya daga cikin abokaina na facebook ya sake posting dinsa a 1/10/2014, shi ya ja hankalina matuka ga yin wannan rubutu na yau, da Najeriya ke murnar cika shekaru 54 da samun yancin cin gashin kai.

Al’amarin da ya girgiza tunani har na sake bibiyar rubutun shi ne, matsalolin da suka dabaibaye kasar nan a shekarar da ta gabata, suna nan jiya eh yau, babu abin da ya canza, sai ma hauhawa da suka yi. Wanda za mu iya cewa ma gwanda jiya da yau. Domin a shekarar da ta gabata lamarin rikicin boko haram ya tsaya ne ga tashe-tashen bom nan da can, da harin dauki daidai jefi-jefi. Amma a yau kungiyar ta samu tagomashin kama gururuwa da dama a jihohin Arewa maso Gabas na karkashin ikon mulkinsu, kuma gwamnati na kallo ta kasa kwato su. Kuma a cikin garuruwan, har da garin su Ahmad Gulak dan gaban goshin Shugaba Jonathan (a da).
Haka ta fuskar ilimi lamarin kara ta’azzara ya yi. A shekarar 2013 a kalla kusan kashi 40 da doriya cikin 100 suka samu nasara a jarrabawar kammala sakandire, amma a wannan shekarar da kyar kashi 30 cikin 100 suka kai gaci. A yayin da a gefe daya yaranmu ‘yan firamare da na sakandire suna zaune a gida cikin halin rashin tabbas bayan karewar hutunsu, sakamakon cutar Ebola da ta yi wa kasar shigar sunkuru, kuma gwamnati ta kasa samar da sahihin tsari na kariya da malamai da iyayen yara za su aminta a koma makaranta a ci gaba da karatun.
Ta fuskar kiwon lafiya nan ma al’amarin kara ta’azzara ya yi. Ban da cutar malaria da ta yi wa al’umma kamun kazar kuku, to har karuwa aka samu ta cutar Ebola ta sanadiyyar sakacin hukumomin kasar nan. Cutar da ta haddasa sanadiyyar rasa rayukan wasu likitoci da malaman jiyya. Kuma ta kara kawo nakasu ta fuskar ilimi, har aka kai fagen da yaranmu suna zaune a gida cikin halin rashin tabbas.
Haka cin hanci da rashawa, shi ma ya yi tashin gwauron zabo a tsakanin hukumomi da al’ummomin kasar nan, inda abin kunya, da Allah wadai, ke ci gaba da faruwa tsamo-tsumo a cikin gwamnatin nan ta mai malafa. A irin hakan ne aka dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), saboda tonon sililin batan dabo da biliyan 20 ta yi a asusun Kamfanin Man fetur na kasa (NNPC). Lamarin da ya zubar da kima da darajar kasar a idon duniya.
Ga fasakwaurin makamai da garkuwa da mutane su ma sai habaka suke, inda a dan tsakanin nan wani abin kunya ya faru da ya girgiza da dama daga dubun-dubatar al’ummomin kasar nan, wato kama jirgin shugaban kungiyar Kiristobi ta Najeriya (CAN) Pastor Ayo Oritsejafor da badakalar safarar makamai a kasar Afrika ta Kudu dauke da kudi Dalar Amurika miliyan 10. Kuma gwamnatin kasar nan ta fito gaba gadi ta amsa tana da masaniya akan badakalar makaman. A yayin da shi kuma shugaban kungiyar CAN a nasa bangaren ke ikirarin ya bayar da jirgin haya. Wanda a iya saninmu, jirgin rijistar pribate jet gare shi. Shin ko yaushe ya koma safarar kasuwanci (commercial jet)?
Haka a shekarar ce aka gudanar da wani abu mai kama da wasan kwaikwayo mai suna “Taron Makomar kasa”. Taron da aka yi asarar miliyoyin kudi a iska gami da kara rarraba kan al’ummomin kasar, da kuma zubar da kimar kasar a idon duniya, duba da yadda aka rika karajin gaya wa juna bakaken maganganu a zauren taron, kafafen labarai na yadawa a duniya jama’a na gani.
Hakika irin abubuwan da suka faru, suna da dimbin yawan da ba za a iya lissafa su ba, sai dai mu yi addu’ar Allah yasa shekarar 2015 ta zo mana da kyakkyawan canji duba da yadda zabe ke kara kusantowa ga hukumar ta INEC, al’ummomin kasar sun dawo daga rakiyarta saboda ta kasa gudanar da sahihin zabe a kasar nan. Amma ta wani bangaren zabukan, irin na Osun da Ekiti, ta yi rawar gani. Sai dai abin da ke ba al’umma tsoro shi ne, yadda hukumar ta INEC tana gani ake amfani da dubban jami’an tsaro, da kame jagororin jam’iyyar adawa, ta yi gum ta kyale taki cewa komai, kamar yadda ya faru a zabukan da suka gabata. Wanda hakan ya saba wa kundin tsarin hukumar dokar zabe ta kasa. Allah ya yi mana sauyin halin muna addu’ar Allah kawo mana kyakkyawan canji, Ya kuma kawo mana karshen wannan mulki na danniya da babakere.
Ahmad A Daura 08032320871

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya