Najeriya a tarihin Gasar Commonwealth

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala gasar Commonwealth a Birnin Glasgow na kasar Scotland. Najeriya ta kasance a matsayi na 8 bayan ta ci Zinariya 11 da Azurfa 11 da kuma Tagulla 14. Jumullar lambobin da Najeriya ta ci shi ne 36. Wannan shi ne karo na biyu da Najeriya ta taka […]

Najeriya a tarihin Gasar Commonwealth

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala gasar Commonwealth a Birnin Glasgow na kasar Scotland.
Najeriya ta kasance a matsayi na 8 bayan ta ci Zinariya 11 da Azurfa 11 da kuma Tagulla 14. Jumullar lambobin da Najeriya ta ci shi ne 36.
Wannan shi ne karo na biyu da Najeriya ta taka muhimmiyar rawa tun bayan da ta fara shiga gasar a shekarar 1950.
Gasar da Najeriya ta fi cin lambobi ita ce, wadda aka gudanar a birnin bictoria da ke kasar Kanada a shekarar 1994, inda Najeriya ta samu Zinariya 11; Azurfa 13 da kuma Tagulla 13, jumullar lambobi 37.
A gasar ta bana Najeriya ta taka muhimmiyar rawa a bangaren daga nauyi, inda ta samu Zinariya 6, Azurfa 6 da kuma Tagulla 1, inda a bangaren wasan Tennis na teburi na ta samu Tagulla 1. Sauran bangarorin da Najeriya ta samu lambobi sun hada da Tsere da Kokawa da Damben Boding.
Wasanni da Najeriya ba ta samu lamba ba sun hada da Ninkaya da Tseren Keke da kwallon Rugby Sebens da kwallon Hockey da kwallon Netball da sauransu.
A gasannin Commonwealth 13 da Najeriya ta samu shiga, ta ci lambobi 212, Zinariya 61; Azurfa 61 da kuma Tagulla 85.
kasashe 34 suka halarci gasar bana, inda aka fafata a kan wasanni 17. An lashe Zinariya 237; Azurfa 237 da kuma Tagulla 302, inda jumullar lambobin da aka lashe ta zama 776.