NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen da iyaye ke fuskanta wajen tarbiyyar ’ya’yansu

Daga cikin manyan sauye-sauyen akwai aikin albashi da iyaye mata ke yi a wannan zamani wanda a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ‘ya’ya suke samu.

NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen da iyaye ke fuskanta wajen tarbiyyar ’ya’yansu

Kula da tarbiyyar yara (2)

Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samo daga wurin iyayensa a da can, irin mu’amalan da ke tsakaninsa da iyaye har ma da shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye.

A yanzu kuwa al’amrin ya canza, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa.

Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen shi ne aikin albashi da iyaye mata ke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ‘ya’ya suke samu.

Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan irin ƙalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyar ’ya’yansu.

Domin sauke shirin, latsa nan