NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen da zai yi wa zaɓaɓɓen Gwamnan Ondo Dabaibayi

Kama daga rikicin cikin gida a jam’iyyarsa ta APC zuwa ga barazanar jam’iyyun adawa da muradun al’ummar da ya yi wa alƙawura, anya zaɓaɓɓen Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, bai sha ta fi cikinsa ba kuwa?

NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen da zai yi wa zaɓaɓɓen Gwamnan Ondo Dabaibayi

Lucky Aiyedatiwa

Tun bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe Zaɓen Gwamna da aka gudanar a Jihar Ondo ranar 16 ga watan Nuwamba, hankula suka karkata zuwa ga ƙalubalen da ke gabansa.

Kama daga rikicin cikin gida a jam’iyyarsa ta APC zuwa ga barazanar jam’iyyun adawa da muradun al’ummar da ya yi wa alƙawura, anya Aiyedatiwa bai sha ta fi cikinsa ba kuwa?

Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari a kan abubuwan da Zaɓaɓɓen Gwamnan na Jihar Ondo ka iya fuskanta bayan ya sha rantsuwar kama aiki.

Domin sauke shirin, latsa nan