NAJERIYA A YAU: Ƙuncin da marasa lafiya suke ciki saboda tsadar magani

Tsadar magunguna a asibiti ta sa marasa lafiya da ’yan uwansu sun koma sayen maganin a hannun masu tallan sa a kafaɗa, ko amfani da maganin gargajiya, ko kuma, a wasu lokutan, haƙura da maganin.

NAJERIYA A YAU: Ƙuncin da marasa lafiya suke ciki saboda tsadar magani

Wani shagon sayar da magunguna (Hoto: Pharmacy network)

Farashin magunguna a asibiti na ci gaba da tashin gwauron zabo a Najeriya, lamarin da ke jefa marasa lafiya da ’yan uwansu cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

A sakamakon haka, marasa lafiya da dama sukan koma amfani da abin da ya fi musu sauki — ko dai sayen maganin a hannun masu tallan sa a kafaɗa, ko amfani da maganin gargajiya, ko kuma, a wasu lokutan, su haƙura da maganin ɗungurungum.

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan halin da marasa lafiya suka shiga a sakamakon tashin gwauron zabo da maganin asibiti ya yi.

Domin sauke shirin, latsa nan