NAJERIYA A YAU: 2023: Yadda Tinubu Ya Karbi Batun Takarar Osibanjo

Tsakanin Tinubu da Osinbajo wa zai samu goyon bayan Fadar Shugaban Kasa?

NAJERIYA A YAU: 2023: Yadda Tinubu Ya Karbi Batun Takarar Osibanjo

Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu

Domin sauke shirin latsa nan

Hankalin ’yan Najeriya ya koma kan yadda Uban Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ke neman takarar shugaban kasa ya ji da fitowar Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osibanjo, takarar kujerar.

Da wace fuska Tinubun ya karbi aniyar ta Osibanjo, wanda ake kallo a matsayin  yaron gidansa? Shin wuyan Osinbajo ya kai yanka? Wadanne kalubale takarar tasa take tattare da su? Sannan tsakanin shi da Tinubu wa zai dagula wa wani lissafi?

Shirin Najeriya A Yau na wannan na tafe gamsassun bayanai.