NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan IPOB Ke Shirin Hana Zabe A Kudancin Najeriya
Bin diddigin wannan batu, tare da tattaunawa da hukumar da masana domin gano bakin zaren
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ‘yan haramtacciyar kungiyar aware ta IPOB ne ke bankawa ofisoshin Hukumar Zabe Ta Najeriya INEC wuta a Kudancin Najeriya.
Shin mene ne yasa ake ci gaba da kone ofisoshin INEC a Kudancin Najeriya, kuma wane irin tasiri hakan zai yi ga yankin a zaben 2023?
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Sayen Zaman Lafiya A Arewa
- DAGA LARABA: Yadda Zubar Da Ciki Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya
Shirin Najeriya A Yau ya bi diddigin wannan batu, ya kuma tattauna da hukumar INEC da masana domin gano bakin zaren.